15-Oct-2025
14-Oct-2025
13-Oct-2025
12-Oct-2025
09-Oct-2025
20251015-Yamai
00:00
1x
Kasancewar mata tushen ginin duk wata al’umma, kuma masu reno da daidaita zamantakewa, ya sa sassan kasa da kasa ke ta aiwatar da manufofi daban daban, na ganin an kyautata rayuwarsu, sun kuma samu ci gaba a dukkanin fannonin rayuwa. A farkon makon nan ma an kaddamar da taron koli na mata na duniya a nan birnin Beijing. Kasar Sin da hukumar MDD mai lura da harkokin da suka shafi daidaiton jinsi, da inganta rayuwar mata ne suka jagoranci taron. Ya kuma hallara shugabannin kasashen duniya daban daban, da jagororin hukumomin kasa da kasa da na shiyyoyi, da jami’an gwamnatoci da dai sauransu.
A bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Botswana. A cikin shekaru 50 da suka gabata, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya bunkasa daga dogaro da albarkatun kasa zuwa karfafa fasahohin zamani. Ban da haka kuma, ana kara samun mutanen kasar Sin da ke gudanar da zaman rayuwa ko aiki a kasar Botswana. A cikin shirinmu na yau, bari mu duba yadda kasashen Sin da Botswana ke yin ayyuka tare don inganta hadin gwiwar zamani, bisa ra’ayin jakadan kasar Sin da ke Botswana mai suna Fan Yong.
A cikin tarihin bil’Adama, mata sun kasance masu kirkiro abubuwan more rayuwa da na al'adu. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, “Idan babu mata, to babu bil'adama, babu al'umma.” “Idan babu 'yancin mata da ci gabansu, to babu 'yancin bil'adama da ci gabansa.” A watan Satumba na shekarar 2015, shugaba Xi Jinping ya jagoranci Taron Kolin Mata na Duniya da aka gudanar a birnin New York, inda ya jaddada muhimmiyar ranar da mata ke takawa, wanda hakan ya janyo matukar cudanyar al'ummar duniya. A yanzu haka, a ranakun 13 zuwa 14 ga watan Oktoba, wato daga yau zuwa gobe Talata, Taron Kolin Mata na Duniya zai sake gudana a nan birnin Beijing, wanda ke jawo hankulan kasashen duniya, wadanda ke jiran samun sabon tunani da kuzari daga jawabinsa.
06-Oct-2025