logo

HAUSA

 • In Ba Ku Ba Gida
 • Sin da Afirka
 • Duniya A Yau
 • Wasannin Motsa Jiki
 • Allah Daya Gari Bambam
 • Mahmooda Taqwa Milad: Mai kiwon tumaki da ta zama malama a jami'a

  Mahmooda Taqwa Milad, ta shafe kuruciyarta a wani kwari da ake kira Do Ab a jihar Vardak dake tsakiyar kasar Afghanistan. Mazauna kauyen sun yi mata lakabi da “Yarinyar da ke zuwa makaranta”.

  A tsakiyar shekarun 1990, Taqwa mai shekaru 7, ta kasance tana doguwar tafiya a hanya mai duwatsu a kowace rana, don zuwa wata makarantar 'yan mata. Kullum tana cikin kadaici, saboda babu wata yarinyar dake zuwa makaranta a kauyensu. Don kawai ta zabi zuwa makaranta, mutanen kauyen sun mayar da ita saniyar ware, kuma ba su yarda 'ya'yansu mata su yi wasa da ita ba.

  Taqwa ta yi karatu na tsawon shekaru biyu kacal a makarantar firamare, sai ta bar makarantar. Lokacin da Taqwa ke hira da ‘yan jaridarmu, tana zaune a kasa, ko tana tunanin ko ta yi shiru, hawaye na zuba a idanunta. Ta ce, bayan wancan lokaci sai ta tattara ganyayyaki a bakin kogi don dumama gida da dafa abinci, gami da kiwon tumaki a tsaunuka. A cewarta, ta zauna a kauyen na tsawon shekaru 9, ciki kuwa ta dauki shekaru 5 tana kiwon tumaki.

  An haifi Taqwa a shekarar 1988. A wancan shekarar, Tarayyar Soviet ta janye sojojinta bayan mamaye Afghanistan na tsawon shekaru 9, daga baya sai Afghanistan ta fada cikin yakin basasa. Bisa wannan halin da ake ciki, wasu mutane sun tsere zuwa kasashen waje, wasu kuma sun buya cikin kauyuka. Mahaifinta, wanda ke koyarwa a Kabul ya rasa aikin yi, kuma babu dabara sai kawai ya gudu tare da iyalinsu zuwa garinsu da ke lardin Vardak. Taqwa ta ce, a lokacin tana karama ba ta iya tuna yawancin abubuwan da suka faru, amma abin da ya burge ta sosai, shi ne iyalinsu suna tashi da karfe 12 na dare, kuma su kan boye a cikin kogo don kada a gano su.

  Taqwa ita ce yarinya mafi kankanta a cikin iyalin, tana da manyan 'yan'uwa 6 da manyan 'yan'uwa mata 3. A yayin da suke zaune a garinsu, wannan babban iyali yana dogaro ne da wata karamar gona don ci gaba da zaman rayuwarsu.

  Makarantar firamare da Taqwa ke karatu tana cikin wani kauye mai nisa. Makarantar 'yan mata ce da kasashen Larabawa suka taimaka wajen ginawa, malama daya ce a makarantar, ita ke koyar da dukkan darussa. Taqwa tana tafiya na dogon lokaci ita kadai a kan hanya mai laka a kowace rana. Lokacin da take gamuwa da mazauna kauyen, su kan ce, "Ga waccan yarinyar da ke zuwa makaranta ..."

  Bayan shekaru biyu tana karatu a makaranta, wata rana ambaliyar ruwa ta afku a wurin, Taqwa ta fada cikin kogi yayin da take tsallake gadar katako, sai dai ta yi sa’a dan uwanta ya cece ta. Amma, tun daga wancan lokacin, iyalinta ba su yarda ta ci gaba da zuwa makaranta ba.

  A watan Oktoban shekarar 2001, Taqwa wacce take kiwon tumaki a kauyen na tsawon shekaru biyar, ta yi amfani da wata dama mai kyau, wato dan uwanta ya koma babban birnin kasar, ita ma ta koma Kabul don ci gaba da karatunta. Amma saboda shekarunta na haihuwa, sai ta nemi shiga aji bakwai kai tsaye, wato aji na farko a makarantar midil.

  Ajin da Taqwa ke karatu yana da rabin rufi ne kadai, kuma akwai dalibai mata 9 a ajin. Malamin su ya taba dukan Taqwa, saboda ba ta iya yin rubutu ba kwata-kwata, sakamakon rashin ilimin asali na haruffa da nahawu. Taqwa tana kuka ta gudu zuwa gida, mahaifinta ya tambaye ta, "Ko dai kina son komawa kauye domin ki rika raka mahaifiyarki, tare da yin aikin gida?" Taqwa ta share hawayenta ta ce "A'a!"

  Taqwa, wadda ke da hazaka kuma mai karfin zuciya, cikin sauri ta cimma nasara a fannin karatu. A cikin jarabawar kammala aji na 7 ta zama ta farko na ajin, a aji 11 wato ajin shekara ta biyu ta makarantar sakandare, ta samu lambar yabo ta fitacciyar daliba. A lokacin kusantowar “Jarabawar shiga jami’a”, hanyar Taqwa wajen shirya jarabawa ita ce, ta bayar da wata sanarwa cewa, ‘Yan matan da ke son yin jarabawar shiga jami’a, da fatan za ku je dakin taro ko wace safiya, kuma zan taimaka muku maimaita darussa na awa daya.

  Bayan ta shiga jami’a, Taqwa ta samu maki mai kyau a fannin karatu, har ta zamo lamba one sau da yawa. Amma, bayan ta kammala karatu a jami’a, sai ta tsaida kudurin zama malama a jami’a, ta gamu da matsaloli masu yawa. Ta ce, ba sa karbar mata a matsayin malamai. Ko da wane yare ko kabila kuke magana, ba a yarda da mata. Ta yi jarrabawa har sau hudu, kafin ta cimma nasara a karo na karshe.

  A yau Taqwa malama ce a Jami'ar Kabul, inda ta riga ta samu digiri na biyu, tana koyar da yare da adabi na Pashto. Tana koyar da daliban aji guda uku a ko wace rana, ko wane aji dake da dalibai a kalla 50. Tana amsa ko wace tambaya daga dalibai ta hanyar amfani da manhajar hira. Ko da yake ta kasance mai shan aiki, ta yadda har ba ta iya amsa sakon sauran mutane, amma tabbas sai ta amsa sakon dalibanta. Tana daukar dalibanta kamar abokanta, kuma ko da yaushe tana kokarin taimaka wa dalibai mata.

  MORE
 • Dr. Mainasara Kogo Umar: Ana bukatar kara hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka

  Barrister Dr. Mainasara Kogo Umar, lauya ne, kana shahararren mai sharhi kan harkokin yau da kullum, kuma masanin harkokin kasa da kasa ne dake birnin Abujan Najeriya.

  A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Dr. Mainasara ya yi tsokaci kan dangantaka da hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, sa’annan a cewarsa, dorawa kasar Sin laifin kwace albarkatu daga Afirka, ko kuma yada jita-jita cewa wai kasar Sin ita kadai, ke cin moriya daga hadin-gwiwar ta da kasashen Afirka, ban da ita Afirka, ba daidai ba ne, kuma abu ne da bai kamata a ce haka ba. (Murtala Zhang)

  MORE
 • Kasar Sin na ba da muhimmanci sosai kan aikin gona da yankunan karkara da kuma manoma

  A ranar 23 ga watan nan na Satumba ne za a gudanar da bikin ranar girbi ta manoman kasar Sin, inda ake sa ran gudanar da shagulgula 3 a bikin na bana a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan, da birnin Jiaxing na lardin Zhejiang da kuma Deyang na lardin Sichuan. Kaza lika akwai karin birane da larduna 11, da za su shiga a dama da su a bikin girbin na bana.

  A shekarar 2018 ne ake fara gudanar da wannan biki a hukumance, bayan da ya samu amincewa daga gwamnatin kasar Sin. Yayin bikin da zai gudana a birnin Changsha na Hunan, za a shirya bukukuwa iri daban daban, a muhimman dandaloli biyu, tare da kananan dandaloli biyu na daban a fadin lardin.

  Wannan dai biki shi ne mafi girma da aka ware domin manoman kasar Sin, wanda ke da nufin karfafa gwiwar manoma, da jinjinawa kwazon su na kirkire kirkiren raya sana’ar su, da ma ba su damar musamman, ta yin murnar manyan nasarori da suka samu a fannin.

  Sanin kowa ne cewa, kaso mafi tsoka na al’ummar Sinawa tun fil azal manoma ne, wadanda gudummawarsu ce ta haifar da ci gaban da kasar ta samu kawo yanzu. Kaza lika, baya ga ciyar da kasa, manoman kasar Sin sun ba da gagarumar gudummawa wajen raya yankunan karkara, ta fannin fadada harkokin tattalin arziki da zamantakewa.

  A hannu guda kuma, bisa tarihi, manoman kasar Sin sun yi rawar gani wajen mara baya ga ayyukan JKS, wadanda suka hada da juyin juya hali, da gina kasa, da aiwatar da sauye sauye.

  Bisa hakan ne ma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, ba za a taba watsi da manoma ba, kana ba za a taba watsi da yankunan karkara ba a kowane irin lokaci.

  Bikin ranar girbi ta manoman kasar Sin, kamar ko wace shekara, a bana ma zai kunshi nuna wasannin gargajiya, da nuna kwarewa a fannin sana’ar ta noma, da kuma dandana nau’o’in abinci daga sassan yankunan kasar ta Sin daban daban. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam/Sanusi Chen)

  MORE
 • Kwallon kafa ta lokacin hutu na baiwa matasan ‘yan kwallo a Kamaru damar kaiwa ga burin su na shiga manyan gasanni

  A birnin Yaounde na kasar Kamaru, lokacin hutun ‘yan makaranta muhimmin lokaci ne da akan ga yara da matasa na sassan kasar daban daban, na ta buga tamaula a filaye masu kura, ana iya ganin yara matasa sanye da riguna kala kala, suna buga kwallo yayin da ‘yan kallo ke shewa.

  Cikin su, Hamza Abdouraman matashi ne dake bayyana burin sa na zama shahararren dan kwallo, wanda zai nunawa duniya kwarewarsa. Duk da cewa yana so da farko ya yi suna a Kamaru, a hannu guda yana fatan kaiwa ga nahiyar turai, kana yana fatan taka leda a kungiyar Manchester United.

  Matashin mai shekaru 26 da haihuwa na cikin yara ‘yan Kamaru masu dinbin yawa, dake fatan yin suna tare da samun arziki ta hanyar taka leda. A lokacin da irin wadannan matasa ke na su kwazon, akwai kuma manajoji, da koci koci dake farautar matasan ‘yan wasa masu basira a kasar

  Kungiyar kwallon kafar da Abdouraman ke takawa wasa, wato “Money FC, na buga wata gasa da ake shiryawa a lokacin hutun ‘yan makaranta, lokacin da wakilin Xinhua ya isa filin wasan da suke buga kwallo.

  A cewar Mouhamadou Aminou, mashiryin gasar, akwai kyaututtuka masu maiko da za a baiwa ‘yan wasan da suka zamo zakaru a gasar. Akwai kuma tanadin gabatar da su ga manyan kulaflika domin su buga wasa a kungiyoyin kwararru, inda daga nan za su iya tsallakawa zuwa manyan kulaflika har da na waje.

  Manyan ‘yan wasa masu buga irin wannan gasa ta lokacin hutun ‘yan makaranta a baya, a yanzu su ne ke daukar nauyin shirya gasar, domin samar da damar horo da kwarewa ga ‘yan baya tun suna kanana.

  A Kamauru kwallon kafa tamkar addini take, don haka mutane irin su Aminou ke shirya gasanni lokacin da yara ke hutu a ko wace shekara, wadda kan baiwa yara har na kauyuka damar shiga a dama da su, lamarin da ke zama wata dama har a birane ta samun nishadi.

  A Kamaru, yara na matukar kaunar wannan gasa, a wasu lokuta akan ga yara ba ko takalmi, daga iyalai daban daban, daga kabilu, da mahangar siyasa daban daban suna wasan kwallo tare.

  Wasu daga irin wadannan yara ‘ya’yan talakawa ne, wadanda ke da burin cimma manyan nasarori a rayuwa ta hanyar kwallo kafa, da fatan hakan zai ba su zarafin taimakawa iyalan su fita daga kangin talauci.

  Idan an dubi tarihi, za a ga cewa, wasu daga shahararrun ‘yan kwallo ciki har da dan wasan da ya taba zama mafi hazaka a nahiyar Afirka har karo 4 wato Samuel Eto'o, da kuma dan wasa mafi hazaka a Afirka cikin shekaru sama da 50 wato Roger Milla, dukkanin su sun fara ne da taka leda a irin wadannan gasanni na lokacin hutun ‘yan makaranta, a kananan filayen dake cike da kura, wasun su ba tare da takalmi a kafafunsu ba.

  Bisa shirin hukumar kwallon kafar Afirka AFCON, kasar Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafar nahiyar da za a buga a badi. Don haka ga yara masu burin cimma manyan nasarori a fannin kwallon kafa, gasar ta hukumar AFCON tana yi musu kaimi, duba da cewa a gasar mai zuwa, taurarin ‘yan wasan nahiyar irin su Mohamed Salah, da Sadio Mane na a Senegal za su hallara.

  Don haka ne ma adadin matasan ‘yan wasa dake halartar gasar a bana ke karuwa, a cewar Louis Tangono, wanda ke horas da kungiyar Mokolo FC. Tangono ya ce "Muna lalubo yaran ‘yan kwallo dake taka leda a nan da can, wadanda kuma ba su da wata alaka da masu shirya gasar. Muna kuma fitar da kwararrun ‘yan wasa matasa daga kungiyoyin kwallon kafar birnin Yaounde.

  Sai dai duk da karatowar wannan gasa, a bangaren kasar ta Kamaru, akwai babban kalubale. Duk da cewa gwamnatin kasar ta kammala ginin katafaren filin wasa na zamani, a shirin ta na karbar bakuncin gasar ta AFCON, a hannu guda, har yanzu unguwanni da yankunan al’ummu marasa galihu ne ke fitar da ‘yan kwallon kasar mafiya yin fice. To sai dai kuma idan an kwatanta da yawan wadanda ke samun cikar burin su a wannan fage, masharhanta na cewa, cikin duk kusan matasa ‘yan kwallo 500, daya kacal ke iya ketarawa har ya kai ga matsayi na bajimta.

  Bugu da kari, ko da ma ‘yan kadan din da kan kai ga samun nasara, kalilan ne ke iya samun damar bugawa manyan kungiyoyi da ke biyan su makudan kudade. Amma duk da haka, matasan Kamaru ba sa watsi da burin su, da mafarki na cimma babban sakamako!

  MORE
 • Manoman kasar Sin sun gudanar da shagulgulan murnar samun girbi mai armashi

  Noma tushen tattalin arziki, kamar yadda bahaushe kan ce.

  A kwanan nan ne, Sinawa a sassa daban daban na kasar suka gudanar da shagulgula na murnar bikin girbi na manoma, bikin da ya fado a jiya Alhamis, ranar 23 ga wata.

  A nan kasar Sin, an ayyana kafa bikin girbi na manoma ne a shekarar 2018, inda aka tsai da kudurin gudanar da bikin a yanayin kaka, lokacin da tsawon rana ke daidai da dare, wato wanda ya kan fado a tsakanin ranar 22 zuwa 24 ga wata, kuma a wannan shekara, an gudanar da bikin ne a jiya 23 ga wata, wato a karo na 4.

  Walikiyarmu Lubabatu ta kuma kawo mana tsaraba daga lardin Hunan da ke tsakiyar kasar, inda aka gudanar da kasaitaccen biki.

  MORE
LEADERSHIP_fororder_微信截圖_20210830184249