Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-03 17:29:18    
An samar da hidima ga 'yan'uwanmu a nan birnin Beijing

cri

Tare da ci gaban da aka samu kan huldojin tsakanin babban yankin kasar Sin da Taiwan,mu'amalar da ake yi tsakanin mutanen birnin Bejing babban birnin kasar Sin da 'Yan'uwanmu na Taiwan a fannin tattalin arziki da al'adu,sai kara yawa take yi a kwana a tashi.Mutanen Taiwan dake nan birnin Beijing suna sa ido kan manyan sauye sauyen da ake samu da kuma harkokin siyasa da zaman rayuwar jama'a a babbar mahaifa,kuma sun dukufa kansu sau da kafa a kai.Daga cikin 'yan'uwan Taiwan a nan birnin Beijing,da akwai wasu sun zuba jari da bunkasa masana'antu,da wasu suna karatu,da wasu suna aiki a fannin bincike ilimin kimiyya da samar da ilimi,har ma da akwai wasu sun saye gidaje sun yi shirin zama nan birnin Beijing cikin dogon lokaci.Ba tare da kula da dalilansu na zama a nan birnin Beijing,Ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin jama'a ta birnin Beijing ya yi iyakacin kokarinsa wajen ba da hidima ga 'yanuwan Taiwan,har ma wasu ma'aikatan ofishin nan sun zama amintattun aminai na 'yanuwan Taiwan.A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wasu labarai dangane da ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin jama'a ta birnin Beijing."Barka da buga waya! Nan ne ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin jama'a na birnin Beijing.Ko kana da wani bukatu?"

Wannan murya mai dadin ji,murya ce da 'yan'uwan Taiwan da dama dake aiki da zama a nan birnin Beijing su kan saba da ita.Lambar wayar tarhon nan ita ce 84080428. Wata hanyar waya ce ta musamman da aka shimfida a shekara ta 2003 musamman domin amsa tambayoyi ko daidaita matsalolin da 'yan'uwan Taiwan suke fama da su a nan birnin Beijing kamar su fannonin zuba jari,da zaman daidai wa daida,da samun inshura,da binciken lafiyar jiki da samu jinya,da nema samun rance,da kan yadda ake samun takardun shaidun da ake bukata da visa,har ma da akwai matsalolin da suke fama da su wajen ayyukansu da zamansu.Miss Lu Hui,wata ma'aikatacciya ce da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin jama'a ta birnin Beijing mai kula da harkokin a wannan fanni,ta yi alfahari da cewa wannan hanyar tarho ta zama wata muhimmiyar hanya da ofishin kula da harkokin Taiwan na Gwamnatin birnin Beijing ke amfani da ita wajen yin cudanya da ketare."A karshen shekara ta 2003 ne,mun buga wani kati domin tafiyar da harkokin waje,wannan shi ne katin samar da hidima ga 'yan'uwan Taiwan.Daga nan mun buga lambayar waya a jikin katin,da haka mutane da yawa sun sami wannan lamba sun kuma bugo mana waya,ciki har da 'yan'uwan Taiwan dake zama a kasashen Ketare,sun bugo mana wayoyi domin neman amsoshi kan tambayoyin da suka gabatar.Daga cikinsu da akwai wasu kararraki da bukatun 'yan'uwan Taiwan na neman kare moriyarsu,lalle wannan wuri ya zama wani reshen ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin birnin Beijing."

A hakika.an shimfida wannan hanyar waya ne bisa wani matakin da ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin birnin Beijing ya dauka a shekarun baya domin kawo sauki ga 'yanuwan Taiwan da ke zama a nan birnin Beijing.Bisa labarin da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya samu,an ce domin kyautata muhallin da 'Yan'uwan Taiwan ke ciki wajen zuba jari da aiki da karatu da zama,ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin birnin Beijing ya tsara ka'idoji 16 da suka shafi harkokin zuba jari da aiki da karatu da yawon bude ido da zama na 'yan'uwan Taiwan a nan birnin Beijing ta yadda 'yan'uwan Taiwan za su iya more kyakkyawar hidima mai amfani a nan birnin Beijing.Ban da wannan kuma ofishin kula da harkokin Taiwa na gwamnatin birnin Beijing ya kuma bude wani shafi na musamman a yanar gizo ta internet da sunan "Beijing ---Taiwan one line",ya kuma dada kyautata shi da sabunta shi duk domin biyan bukatun 'yan'uwan Taiwan wajen samu labaru da bayanai dangane da duniya da tattalin arziki da ciniki da zaman rayuwa da kuma manufoffi da ka'idoji.Haka kuma ya wallafa da buga wani karamin littafi mai lakabi "labarai da bayanai masu amfani ga "yan'uwan Taiwan da suka zo nan birnin Beijing" duk domin ba da hidima ga 'yan'uwan Taiwan na zama a nan birnin Beijing wajen zuba jari da karatu da zama da yawon shakatawa a nan birnin Beijing.

Ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin birnin Beijing ya kuma kafa wata cibiyar samar da hidima ga 'yan kasuwa na Taiwan wajen zuba jari karkashin gwamnatin birnin Beijing da "wata cibiyar daidaita kararrakin da'yan kasuwa na Taiwan suka kawo karkashin ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin birnin Beijing duk domin kara inganta tsare tsaren ba da hidima ga 'yan kasuwan Taiwan wajen zuba da jari da da daidaita kararrakin da suka kawo,ta haka aka samu hanyoyi da dama da ke kula da kararrakin da 'yan kasuwa na Taiwan suka gabatar da kuma amsa tambayoyin da suka kawo dangane da harkokin Taiwan.Mr Zhou Hengzhao,wani jami'I ne na cibiyar daidaita kararrakin da 'yan kasuwa na Taiwan suka kawo karkashin ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin birnin Beijing.Aikinsa a kowace rana shi ne daidaita kararrakin da suka shafi moriyar 'yan'uwan Taiwan kai tsaye.

Ya ce  "kararrakin da 'yan kasuwa na Taiwan suka kawo sun kasu wasu gidaje:na farko gardama kan kwangila;na biyu gardama kan nauyin da kowane bangare ya dauka.yawancinsu harkokin ne na tsakanin jama'a,wasu kuma sun shafi tsare tsaren hukumomi,ko kan takardun zartaswa da takardun shaidu,da kuma akwai batun shari'a na daukaka kara da yanke hukunci,kan hukuncin da aka yanke,bangarori biyu masu bambanta da juna,da kuma batun aikata laifuffuka." Ali)