Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 19:21:46    
Zaman rayuwar mutanen kauyen Jiamu da suke da zama a cikin sabbin gidaje

cri

Jama'a masu karatu, ana kiran jihar Tibet mai cin gashin kanta "Rufin Duniya". Ana kuma kiran shiyyar Ali da ke yammacin jihar Tibet cewa "Tana kan rufin duniya". A shiyyar Ali inda matsakaicin tsayinta ya kai mita 4500 daga leburin teku, manoma da makiyaya suna shan wahala sosai. Amma tun daga shekarar da ta gabata, bayan da aka soma gina sabbin gidaje domin manoma da makiyayi na shiyyar, gwamnatin kasar Sin ta zuba kudade da yawa domin gina musu sabbin gidaje. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ku zuwa wani kauye mai suna Jiamu domin sanin yadda 'yan kabilar Tibet suke da zama a cikin sabbin gidajensu.

Kauyen Jiamu yana nesa da garin Shiquanhe, wato hedkwatar shiyyar Ali ta jihar Tibet da kilomita 20. Lokacin da wakilanmu suke ziyara a kauyen, sun ga sabbin gidajen kabilar Tibet, wasu daga cikinsu suna da banaye biyu, kamar villa ne masu inganci. Wakilanmu sun ji mamaki sosai. Mr. Gamaciren, shugaban kauyen Jiamu ya ce, ai yau da shekara 1 da ta wuce, babu kome a wannan wuri, manoma da makiyaya sun yi zama a cikin tsaunuka. Amma a watan Afrilu na shekarar 2006, gwamnatin kasar Sin ta zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Renminbi yuan miliyan 4 da dubu dari 1 domin gina wa manoma da makiyaya sabbin gidaje. Gamaciren ya ce, "Akwai gidaje 57 tare da mutane 279 a cikin kauyenmu. Suna neman kudi ne ta hanyar kiwo da yin cirani a sauran wurare. Kafin mu zo nan, mun gina gidajenmu ne da kasa. Bayan da gwamnatin ta aiwatar da ayyukan samar wa manoma da makiyaya sabbin gidaje, yanzu mazaunanmu sun samu sabbin gidaje."

Gamaciren ya gaya wa wakilanmu cewa, jimlar fadin sabbin gidajen da aka gina ya kai muraba'in mita kusan dubu 5. Lokacin da ake gina sabbin gidaje, gwamnatin kasar Sin ta samar da wasu kudin rangwame, mutumin da ke son gina sabon gida ma ya kebe wasu kudade daga aljihunsa. Gwamnatin tana samar da kudin rangwame ne bisa yawan iyalan wani gida, idan kudaden da gwamnatin ta samar ba su isa kudin da ake bukata ba, sai mutumin da ke son gina sabon gida ya zuba da kansa.

A da, mutanen kauyen Jiamu sun yi zama a cikin kananan gidaje masu duhu sosai. A cikin irin wannan tsohon gida, akwai dakin kwana guda tare da zaure daya da wani karamin dakin dafa abinci. Labadunzhu, wani dan kauyen Jiamu ya ce, a da, yana kuma son gina wani sabon gida, akwai ba shi da isashen kudi. Amma yanzu, an riga an kusan kammala aikin gina sabon gidansa da fadinsa ya kai fiye da muraba'in mita dari 1. Lamadunzhu ya gaya wa wakilanmu cikin harshen Tibet cewar, "An kashe kudin Renminbi yuan dubu 50 domin gina wannan sabon gida. Amma na kebe kudin Renminbi yuan dubu 10 kawai daga aljihuna, gwamnati ne ta samar mini sauran kudaden da nake bukata. Yanzu, an kusan kammala shi. A da, ni da iyalina mun yi zama a cikin wani karamin gida kawai."

Ba ma kawai mutanen kauyen Jiamu suna jin dadin sabbin gidajensu ba, har ma suna jin dadin shirye-shiryen talibijin da wayar salula da rediyo. Yanzu suna cikin sauki wajen yin mu'amala da sauran wuraren duniya. Labadunzhu da matarsa Cirenyangzong suna da wata yarinya, yanzu tana karatu a jihar Xinjiang. Da wakilanmu suka kai ziyara a gidansu, malama Cirenyangzong ta buga waya ga diyyarta domin gaya mata wannan labari. Malama Cirenyangzong ta ce, Lokacin da take gina wa manoma da makiyaya na shiyyar Ali sabbin gidaje, gwamnatin wurin tana kuma nazarin hanyoyin neman kudi domin manoma da makiyaya. Gamaciren, shugaban kauyen Jiamu ya ce, gwamnatin ta sa kaimi kan matasa da su je jihar Xinjiang domin koyon fasahar kiwon kaji. A waje daya, kwamitin kauyen yana da shirin tara dukkan motocin daukar kaya domin sufurin kayayyaki. Amma, a ganin Gamaciren, abin da ya fi farin ciki shi ne, an riga an kusa kammala raya wani sansanin kiwon shanu da tumaki da gwamnatin wurin ta samar da kudin gina shi. Za a iya soma amfani da shi ba da jimawa ba.

"Yanzu muna da wani sansanin kiwon shanun nono da wani sansanin kara kibar shanu da tumaki. Yanzu an riga an kammala aikin share fagen kafa shi, tun daga lokacin kaka, za mu sayi shanu da tumaki da makiyaya suke kiwo domin kara kibarsu." (Sanusi Chen)