Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-22 20:28:59    
Aikin bajinta da Mr. Wang Youde, dan kabilar Hui ya yi don hana kwararowar hamada

cri

A jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin, akwai wani mutum dan kabilar Hui kuma mai matsakaitan shekaru mai sunan Wang Youde, wanda ya shafe shekaru fiye da 20 yana shugabantar ma'aikatan hukuma da ma'aikata na gundun daji domin dasa bishiyoyi cikin hamada mai fadin fiye da kadada dubu 20.

A shekarar 1985, Mr. Wang Youde mai shekaru 30 kawai a wancan lokaci ya je aiki a gandun daji mai sunan Baijitan da ke birnin Lingwu na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta, kusan an ce ba a samu girbin amfanin gona ko kadan sabo da kwararowar hamada mai tsanani da aka yi a can, kuma manoma sun yi kaura daga wurin ala tilas domin gudun babbar iska da rairayi. Mr. Wang Youde ya tuna da cewa,

"A da, idan an dasa itatuwa masu ba da 'ya'ya ko kuma an shuka amfanin gona, amma ba a samu 'ya'yan itatuwa da amfani gona ba sabo da kwararowar hamada, kwararowar hamada ba ma kawai ta jawo illa ga mutane ba, haka ma ga amfanin gona sosai."

A wancan lokaci, gandun daji na Baijitan ya kasance da talauci da rashi, ba kamar kyakkyawan halin da Mr. Wang Youde ya zata ba, ma'aikatan gandun daji sun yi ragwan aiki, matsakaicin yawan kudin shiga da kowanensu ya samu ya kai kudin Sin wato Yuan darurruwa kawai, shi ya sa yawancinsu suna nemen badalinsu zuwa sauran wurare. Ko da yake da akwai matsaloli da yawa da ke gaban Mr. Wang Youde, shugaban gandun daji kuma saurayi, amma bai durkusa a gaban wahalolin ba, maimakon haka sai ya fara yin gyare- gyare da kuma daidaita harkokin gandun daji.

A shekarar 1985, kuma a karkashin shugabancin Mr. Wang Youde ne, gandun daji ya kaddamar da jerin matakan gyare-gyare, ciki har da daukan ma'aikata kadan amma mafi kyau da samun saukakkiyar hukuma, ma'aikatan kuma suna samun rabonsu gwargwadon yawan aikin da suka yi. Gyare-gyaren da aka yi ya kawo karfin zuciya ga ma'aikatan gandun daji na Baijitan, wadanda suka yi tukurun aiki ba dare ba rana wajen dasa itatuwa da sauran harkoki.

A shekarar da Mr. Wang Youde ya fara yin gyare-gyare a gandun daji, fadin gandun daji da aka kirkiro ya kai kusan kadada 400, jimlar tsabar kudin da aka samu ta wuce Yuan dubu 90, hakikanan abubuwa sun tabbatar da cewa, irin wannan dabarar da aka dauka ta hanyar kimiyya wajen dasa bishiyoyi don tare iska da rairayi ta sa kaimi ga ma'aikata wajen aikinsu sosai. Mr. Wang Youde ya ce,

"Hakikanin abu na gaskiya shi ne, a da dukkan mutane ciki har da ma'aikata da ma'aikatan hukuma, dukkansu sun bayyana cewa, da akwai babban matsin lambar da aka yi musu wajen dasa itatuwa don tare iska da rairayi, amma yanzu suna jin dadi bayan da suka cim ma manufar tattalin arzikin bola jari. Ina ganin cewa, muddin ka kudura niyya ka yi gyare-gyare, kuma ka ba da karfin gwiwa ga ma'aikata wajen dasa itatuwan tuffa da sauran amfanin gona na sayarwa, bayan da ma'aikata suka kara samun kudin shiga da yawa, dukkansu sun ji dadi".

Idan an yi magana kan aikin dashen bishiyoyi don tare iska da rairayi a baka yana da sauki, amma a hakika yana da wahaloli da yawa. A farkon lokacin hunturu na shekarar 1992, an ba da umurni ga gandun daji na Baijitan domin dasa itatuwa a wurin hamada mai sunan Daquan, domin kammala wannan aiki, Mr. Wang youde yakan yi barci awoyi 3 zuwa 4 kawai a kowace rana, da dare kafafuwansa sun kumbura har bai iya cire takalmansa ba, kuma ya kamu da ciwon hanji da sauran cututtuka fiye da 10, amma bai taba sunkuyar da kansa a gaban wahaloli ba, ya ce,

"Hamada ta jawo babbar illa ga gonaki da gidajen fararen hula da kuma koguna, sa'an nan kuma da akwai manyan hanyoyin mota 4 da hanyoyin dogo 2 wadanda suka ratsa hamada ta wannan wuri, shi ya sa dashen bishiyoyi ba ma kawai zai iya ba da kariya ga albarkatun tsire-tsire da na dabbobi ba, muhimmin abu shi ne domin ba da kariya ga hanyoyin mota da hanyoyin dogo da Rawayen kogi da kuma birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia."