Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 14:17:18    
Mahayiya Liu Lina da ke filin gasar wasannin Olimpic

cri

A gun gasar wasannin Olimpic ta Beijing wadda aka rufe kwanan baya, da akwai wata kyakkyawar budurwa ta kasar Sin wadda ta shiga gasar rawar dawaki wato nuna fasahar hau kilisa kuma sanye da tufafi masu kyau wadda aka yi a birnin Hong-kong, ita ce Liu Lina 'yar kabilar Rasha wadda ta fito daga jihar Xinjiang ta kasar Sin. Jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani game da wannan mahayiyar kasar Sin da ke filin wasannin Olimpic.

Budurwa Liu Lina ita ce 'yar wasa ta farko da ta samu iznin shiga gasar wasannin Olimpic cikin tarihin kungiyar wasan dawaki ta kasar Sin. A shekarar 1994, budurwa Liu Lina wadda take da shekaru 14 a lokacin wata 'yar wasan jefa mashi ce ta kungiyar guje-guje da tsalle-tsalle ta kolejin wasan motsa jiki ta jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin. A lokacin kuwa Mr. Ban Zhiqiang, mataimakin shugaban kungiyar wasan dawaki ta jihar ya sa ido kan budurwa Liu kuma ya shigar da ita cikin kungiyar domin tana son sukuwar dawaki, daga nan ne ta kama hanyar wasan dawaki, ta ce,

"Ina jin cewa, idan na sa kwat mai wutsiya da farar riga domin wasan dawaki, sai na zama mai fankama da kyakkyawa, dokina kuma yana da kyaun gani, wasan dawaki yana da babbar ma'ana kuma da sha'awa kwarai".

Ko da yake budurwa Liu tana son wasan dawaki, amma a farkon lokaci tana jin tsoron dawaki masu tsayi kuma masu dogo. Bayan 'yan kwanakin da ta shiga cikin kungiyar wasan dawaki, an aike da ita tare da wasu abokanta zuwa kasar Kirgystan domin koyon fasahar wasan dawaki. Ko da yake tana da shekaru 15 da haihuwa kawai kuma ta sha wahaloli da yawa wajen tattaba wasan, amma ta yi hakuri, ba ta taba yin koke-koke ba, sabo da haka malaman koyarwa na wasan sun gamsu da ayyukan koyon da ta yi sosai.


1 2 3 4