Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-26 15:45:19    
Kasar noma ta kan tuddai--Matsugunar 'Yan Kabilar Hani

cri
Masu saurare, a kan manyan tsaunukan dake yankin kudu maso yammacin kasar Sin, akwai filin noma a kan tuddai mai fadin gaske, inda 'yan kabilar Hani ke zaune zuriya bayan zuriya. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da dangantakar kut da kut tsakanin zaman rayuwar 'yan kabilar Hani da kasar noma ta kan tuddai.

Kabilar Hani, wata karamar kabila ce mai tsawon tarihi a kasar Sin, yawan mutanenta ya zarce miliyan 1.2. Akasarin 'yan kabilar Hani suna zaune a yankunan tsaunuka da tsayinsu ya kai mita 800 zuwa 2500 daga leburin teku. Tun fil azal, 'yan kabilar Hani na kara samun ilimi kan yadda suke gudanar da aikin huda a filin noma kan tuddai.

Saboda akwai albarkatun kasa iri daban-daban a kan tuddai, 'yan kabilar Hani su kan jawo wadataccen ruwan rafi zuwa filayen noma domin yin ban ruwa. Zuwa farkon yanayin bazara, kasar noma tana cike da ruwa mai tsabta, yayin da hasken rana ke sheki, akan ga walwalin kan ruwa. A watan Maris da Afrilu kuma, launin kasar noma ya kan sauya zuwa kore shar, kamar dardumar dake shimfide a kasa. A lokacin karshen yanayin zafi zuwa farkon yanayin kaka, ana yin girbi mai armashi a filin noma kan tuddai.

Tsoho Zhang Youfu, jagoran harkokin addu'a a kauyen Qingkou na garin Xinjie na gundumar Yuanyang ta lardin Yunnan, ana kiranshi "Mi Gu" a yaren kabilar Hani. A matsugunar kabilar Hani, "Mi Gu" kamar gada ce dake yin mu'amala da cudanya tsakanin dan Adam da ubangijinsa. A yanayin bazara na kowace shekara, "Mi Gu" ya kan rera waka domin bude "kofar filin noma kan tuddai", sa'annan mazauna kauyen zasu iya dasa tsuron shinkafa a filin noma kan tuddai.

Zhang Youfu ya dade yana zaune a kauyen Qingkou har tsawon rayuwarsa. Da zaran an shiga cikin kauyen, abun farko dake burge jama'a shi ne hamshakiyar kasar noma ta kan manyan tuddai, wadda ke renon 'yan kabilar Hani zuriya bayan zuriya. A kowace rana da sassafe, Zhang Youfu da dansa Zhang Fuliang su kan je wurin dake da tazarar kilomita 2 ko fiye domin duba tsuron shinkafa da suka dasa a 'yan kwanakin da suka gabata.

Masu saurare, idan kuna yawo kan gefunan magudanar ruwa, za ku gano cewa, a mahadar magudanar ruwa da filin noma a kan tuddai, akwai wasu katakwaye da aka ajiye a tsakiyar magudanar ruwan. Zhang Youfu ya ce:

"Ana kiransu 'Mu Ke', ana yin amfani da wadannan katakwaye domin rarraba ruwan da akan jawo daga rafi. Idan ba'a yi amfani da irin wadannan katakwaye ba domin raba ruwa, ruwan da aka yi amfnai da shi a filin noma a kan tuddai dake kurkusa da magudanar ruwa zai yi yawa, amma ruwa a kasar noma dake nesa da magudanar ruwa ba zai isa ba. Shi ya sa kakannin-kakannin kabilar Hani suka kirkiro irin wannan dabara domin yiwa filin noma a kan tuddai ban ruwa."

Bayan minti 20 ko fiye, Zhang Youfu tare da dansa sun isa kasar noma ta kan tuddai, inda Zhang Youfu ya gabatar mana da al'adun gargajiya na kabilar Hani dangane da filin noma a kan tuddai.

"Ba za'a iya raba zaman rayuwar kabilar Hani da filin noma kan tuddai ba. Muna da wata al'adar gargajiya, wadda ake kiranta 'O'adu' a yarenmu. Idan aka haifi jariri, ba za'a iya fitar da shi daga gida ba sai bayan kwanaki 13. Lokacin da ake fitar da jaririn daga cikin gida, kamata ya yi a ajiye wata sanda a kofar gida, sa'annan a rataya wata hula da wata jaka a kanta."

Tsoho Zhang Youfu ya koma gida da karfe 12 da rabi da tsakar rana bayan da ya kammala rangadinsa a kasar noma ta kan tuddai. Ko da yake ya zarce shekaru 60 da haihuwa, zuciyarsa tana tare da kasar noma ta kan tuddai a kowane lokaci. Zaman rayuwar kabilar Hani na tare da kasar noma ta kan tuddai. A lokacin kuruciyar 'yan kabilar, su kan yi wasanni a wuraren dake kusa da kasar noma ta kan tuddai, lokacin da suka balaga, budurwa da saurayi su kan nunawa juna soyayya a gidajen dake kusa da filin noma a kan tuddai, har ma a lokacin da wani dan kabilar Hani ya rasu, akan ajiye gawarsa a kan tuddai, domin sa ido kan kasar noma har abada.

A halin yanzu, kasar noma ta kan tuddai ginshiki ce ga zaman rayuwar kabilar Hani. Kasar noma ta kan tuddai da fadinta ya zarce kadada dubu 10 har yanzu dai tana renon 'yan kabilar Hani masu dimbin yawa. Domin kiyaye kasar noma ta kan tuddai mai tsawon tarihi yadda ya kamata, a shekarar 2000, an kafa wani sashi na musamman a yankin Honghe mai cin gashin kansa na kabilun Hani da Yi, a wani kokarin gabatar da sunan "kasar noma ta kan tuddai ta kabilar Hani" don ta zama daya daga cikin abubuwan tarihi ta fannin al'adu da aka gada daga kakannin-kakanninmu a duniya. Yanzu, kasar noma ta kan tuddai ta kabilar Hani ta riga ta shiga cikin takardar jerin sunayen abubuwan tarihi ta fannin al'adu da aka gada daga kakannin-kakanninmu guda 35 da gwamnatin kasar Sin ta bullo da ita, haka kuma ta samu tallafin kudi na musamman daga wajen gwamnatin kasar Sin. Shugabar hukumar kula da harkokin filin noma a kan tuddai ta kabilar Hani ta yankin Honghe mai zaman kansa, Madam Zhang Hongzhen ta ce:

"Bisa hazikanci da hazaka da 'yan kabilar Hani suke nunawa, ya kamata su gina birane. Amma har yanzu ba su gina ba. A cikin shekaru dubbai da suka gabata, 'yan kabilar Hani ba su gina birane ba, sun yi dandazo cikin kauyuka. Amma 'yan kabilar Hani suna sa himma da kwazo wajen raya filin noma a kan tuddai. "