Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 22:06:09    
Bayani kan bukin Gexu a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin

cri

Masu saurare, in ba ku mance ba, a cikin shirinmu na makon da ya gabata ne, muka gabatar muku da wani bayani dangane da bukin masoya na 'yan kabilar Li, wanda a kan shirya a ranar 3 ga watan Maris na kowace shekara bisa kalandar noma ta kasar Sin. To, a wannan rana kuma, 'yan kabilar Zhuang dake zaune a jihar Guangxi dake kudu maso yammacin kasar Sin su kan shirya nasu bukin gargajiya, wato bukin Gexu. Masu saurare, a cikin shirinmu na yau, bari mu je gundumar Wuming ta jihar Guangxi, mu ga yadda 'yan kabilar Zhuang suke nasu bukin gargajiya na Gexu.

Masu saurare, yanzu a gundumar Wuming, 'yan mata da samari dukkansu gwanaye ne a fannin kade-kade. A cikin wakokin da suka rera, 'yan kabilar Zhuang su kan nuna sahihiyar zuciya ga juna. Wani dan kabilar Zhuang dake wurin, Qin Heng ya ce:"A gundunar Wuming ta jihar Guangxi, akwai kyakkyawar al'ada ta rera da sauraren wakoki. A duk yayin bukin Gexu, a kan samu halartar dubun dabatar mutane, inda su kan rera waka tare."

1 2 3