Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 16:32:29    
Majalisar wakilan Amurka ta zartas da shirin doka kan yin gyare-gyare kan tsarin inshorar kiwon lafiya

cri
Ran 7 ga wata da daddare, a majalisar wakilan kasar Amurka, an zartas da shirin doka kan yin gyare-gyare kan tsarin inshorar kiwon lafiya bisa dan rinjaye. Wannan ya nuna cewa, an taka hakikanin mataki a fannin yin gyare-gyare kan tsarin inshorar kiwon lafiya da Mr. Obama ya gabatar.

A cikin kada kuri'ar da aka yi a majalisar wakilan Amurka a wannan rana, 'yan majalisar 220 sun amince da shirin dokar, a yayin da wasu 215 ba su amince da shi ba. Kusan dukkan 'yan majalisar da suka fito daga jam'iyyar Republican ba su amince da shirin dokar ba.

Bayan da aka kada kuri'ar, madam Nancy Pelosi, shugabar majalisar wakilan Amurka ta bayyana cewa, wannan shirin doka zai taka rawa mai zurfi kan zaman rayuwar Amurkawa, kamar yadda aka zartas da shirin dokar ba da tabbaci ga jama'a a shekarar 1935. Sa'an nan kuma, Harry Reid, jagoran 'yan jam'iyyar Dimokuradiyya a majalisar dattijai ta Amurka shi ma ya ba da sanarwar cewa, bisa kuri'un da aka kada a majalisar wakilan Amurka, majalisar dattijan kasar ta fahimci aniyar mutane ta yin gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya. Haka kuma, yana ganin cewa, ba da dadewa ba za a samu ci gaba wajen yin gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya.(Tasallah)