Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 20:59:28    
Sin ta halarci taron ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na kasashe mambobin kungiyar G20

cri
Ran 7 ga wata, a tsohon garin St. Andrews na kasar Scotland, an kammala taron ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na kasashe mambobin kungiyar G20, ciki har da Xie Xuren, ministan kudi na kasar Sin da Zhou Xiaochuan, shugaban bankin tsakiya na kasar Sin.

A yayin taron, Xie Xuren ya nuna cewa, ya zuwa yanzu yana kasancewa da abubuwan rashin tabbaci a fannin farfado da tattalin arzikin duniya, ta haka ya kamata kasashen duniya su ci gaba da aiwatar da manufofin tattalin arziki ba tare da kasala ba daga manyan fannoni. Kamata ya yi kasashen da aka mayar da kudinsu a matsayin kudin ajiyewa su tabbatar da darajar kudinsu da darajar musayar kudi. Ban da wannan kuma, ya kamata kasashen duniya su sa muhimmanci kan harkokin kudi da bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa, su dauki matakai cikin lokaci domin daidaita da yin rigakafin aukuwar barazanar da ba ta bayyana ba tukuna, da yaki da samar da kariya ta mabambantan hanyoyi.

Kazalika kuma, rikicin da kasashen duniya suke ta samu ya bayyana a yayin taron. Dangane da manyan tsare-tsare kan daina shirin sa kaimi kan tattalin arziki, Gordon Brown, firayim ministan kasar Birtaniya da Christine Lagarde, ministar tattalin arziki da harkokin kudi da samun aikin yi ta kasar Faransa suna ganin cewa, ya fi kyau a ci gaba da aiwatar da manufofin da suke ba da taimako wajen farfado da tattalin arziki kafin a tabbatar da hakikanin farfadowar tattalin arziki. Amma kasashen Amurka da Japan da Jamus da wasu kasashen da tattalin arzikinsu ya samu farfadowa suna son sa aya ga shirin sa kaimi kan tattalin arziki cikin sauri.(Tasallah)