in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta hada kan sauran kasashen duniya domin yin kokarin neman ci gaban tattalin arziki tare
2009-11-15 12:35:10 cri

A ran 15 ga wata a kasar Singapore, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta hada kan sauran kasashen duniya domin tinkarar kalubalolin da ke kasancewa a gabansu da neman amincewa da juna da neman ci gaban tattalin arziki cikin daidaito ba tare da tangarda ba. A waje daya, kasar Sin tana goyon baya kan yadda ake ci gaban tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban kamar yadda ake fata da tinkarar sauye-sauyen yanayin duniya cikin hadin gwiwa da raya tattalin arzikin shiyya-shiyya bai daya da kuma fama da barazana da ba irin ta gargajiya ba tare.

A wannan rana, Mr. Hu Jintao ya halarci zagaye na biyu na taron kwarya-kwarya na shugabannin kungiyar APEC karo na 17 da aka yi a kasar Singapore, kuma ya bayar da wani muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Mr. Hu ya shawarci kungiyoyin tattalin arziki daban daban da su dauki kwararan matakai masu amfani da kuma kara mai da hankali kan yadda za a sa kaimi ga mutanen da su kara kashe kudi da raya bukatun da ake da shi a kasuwannin cikin gida. Sannan dole ne a tsaya tsayin daka kan matsayin tabbatar da ganin an yi cinikayya da zuba jari a duk duniya cikin 'yanci kuma cikin daidaito ba tare da kowane irin shinge ba domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba daga dukkan fannoni. Sannan a lokacin da ake farfado da tattalin arziki, ya kamata a kyautata tsarin makamashin da ake amfani da shi da kyautata tsarin sana'o'i da kuma kara karfin raya tattalin arzikin bola jari domin neman ci gaba ba tare da tangarda ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China