in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai na kasar Sin suna murnar babbar sallah
2009-11-28 16:35:05 cri
Ran 28 ga wata, babbar sallah ce ga musulmai wadanda suke zaune a wurare daban daban na duk duniya. Sabo da haka, musulmai fiye da miliyan 20 wadanda suke zaune a wurare daban daban, ciki har da jihar Ningxia da ta Xinjiang da birnin Beijing bi da bi ne suka taya murnar wannan babbar sallah a masallatai.

A jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, inda musulmai sun fi yawa a kasar Sin, musulmai sun sanya kyawawan tufafi, kuma sun shiga masallatan da ke wurare daban daban na jihar sun yi sallah domin neman fatan alheri. Bisa wani labarin da aka bayar, an ce, motocin taksi kusan dari 3 na birnin Urumchi, babban birnin jihar Xinjiang, sun yi sufurin fasinjoji ba tare da karbar kudi ba a wannan ranar murnar babbar sallah.

A jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, inda musulmai fiye da miliyan 2 suke zaune, musulmai sun yi sallah kuma sun yanka tumaki domin murnar wannan babbar sallah.

Haka kuma a babban masallacin dake titin Niujie, wato masallaci mafi girma a nan birnin Beijing, musulmai fiye da dubu 6 wadanda suka zo daga kasashe daban daban sun yi sallah domin murnar wannan babbar sallah. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China