in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan ranar yaki da jahilci ta duniya
2010-08-25 19:50:49 cri
Masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Da fatan kuna ilmantuwa daga shirye-shiryenmu. A cikin shirinmu na yau, za mu fara da karanto wasu wasikun da muka samu daga wajenku. Da farko ga wannan sako daga malam Ishaq Abdullahi Bena a Nijeriya, inda ya bayyana cewa, "Ina taya 'yan uwa musulmin duniya barka da shigowar watan Ramadan na wannan shekara, da fatan samun alherin dake cikin wannan wata. Allah ya sada mu da shi, shairin da ke cikin wannan watan. Allah ya nisanta mu da shi, ya kuma kara hada kawu nan musulmin duniya a duk inda suke domin ci gaban addinin Islama baki daya, amin."

To, mun gode, malam Ishaq. Mu ma muna taya musulmin kasa da kasa barka da Ramadan. Da fatan dukkanku za ku samu karuwar lafiya, dukiya, wadata, da kuma kwanciyar hankali. Allah ya taimake mu, amin.

Sakon malam Ishaq ke nan. Bayan haka, a kwanan baya, mai sauraronmu a yau da kullum malam Bello Gero a Sokoto, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Ina mai nuna rashin jin dadina tare da isar da ta'aziya ga al'ummar da suka sami kansu a cikin bala'in ambaliyar ruwan sama a ko ina a duniya, musammam ma kasar Sin da kuma takwaranta Pakistan. Ina mai tausaya musu tare da fatan duk sauran kasashen duniya za su mai da hankali wajen ba da taimako, tare da fatan Allah ya kawo muku sauki, amin."

To, malam Bello, muna maka godiya sosai. Yanzu ana samun bala'u masu tsanani iri daban daban a duniya, kamar ambaliyar ruwa, gangarowar duwatsu da laka, girgizar kasa da dai sauransu. A wasu wuraren kasar Sin kuma, mutane da yawa sun rasu a sakamakon haka. Muna fatan duk kasahen duniya za su kara mai da hankali kan kiyaye muhalli, ta yadda za a samu damar kaucewa sake abkuwar irin wadannan bala'u. Da fatan mutanen dake fama da bala'un za su samu damar farfado da gidajensu.

Sakon malam Bello ke nan. Bayan haka, bari mu karanto wannan sako daga malam Mohammed Idi Gargajiga a Nijeriya, inda ya bayyana cewa, "Zuwa ga filin 'Kananan kabilun kasar Sin' na malama Lubabatu ta sashen Hausa na CRI. Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan allheri da kuma fatan kina cikin halin koshin lafiya, kamar yadda nake a nan Nigeria lafiya. Allah ya sa haka amin. Domin jin dadin shirin kananan kabilun kasar Sin da kike gabatarwa a kowace ranar litinin tare da sha'awar kara sanin tarihi da al'adun kasar Sin da jama'arta baki daya, saboda haka ina so ki bani cikakken tarihin jihar Tibet."

To, malam Muhammed, muna maka godiya sosai sabo da sauraron shirye-shiryenmu da kake yi. Malama Lubabatu ta riga ta karanta wasikarka, kuma ta yi alkawarin gabatar muku da cikakken tarihin jihar Tibet da dai sauran jihohin kasar Sin baki daya. Da fatan za ka ci gaba da mai da hankali kan wannan shiri. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

To, jama'a masu karanta, sakon malam Muhammed ke nan. A kwanan baya, malam Musa Adamu a Katsina, tarayyar Nijeriya ya aiko mana da tambayar cewa, "Don Allah ko za ku ba da wani bayani kan ranar yaki da jahilci da za ta zo nan ba da dadewa ba?" To, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya.

An kafa ranar yaki da jahilci ta duniya ta kasance ranar 8 ga watan Satumba na kowace shekara a babban taron wakilan kungiyar UNESCO a karo na 14 a ran 17 ga watan Nuwamba na shekarar 1965. Makasudin hakan shi ne sa kaimi ga kasa da kasa da hukumomin duniya da su dora muhimmanci kan lamarin, a kokarin yaki da jahilci yadda ya kamata, tare da sa kaimi ga sha'anin tarbiyya a duniya, ta yadda za a cimma burin yin musayar ra'ayoyi tsakanin jama'ar kasa da kasa, da rage bambanci tsakaninsu, da kuma kara yada al'adu da bunkasa zamantakewar al'umma.

Kungiyoyi da dama na gwamnatocin kasa da kasa da na shiyya-shiyya sun kafa kungiyoyin yaki da jahilci, kuma sun gabatar da rahotanni ga jama'a domin fadakarwa kan muhimmancin lamarin, yin nazari kan sakamakon da aka samu a wannan fanni, da kuma kara yin nazari kan hanyoyi da matakan da za a dauka na yaki da jahilci.

JKS da gwamnatin kasar Sin suna dora muhimmanci sosai kan aikin yaki da jahilci, musamman ma a wasu wuraren dake iyakacin kasa. A kowace shekara, su kan tura rukunin yaki da jahilci zuwa wadannan wurare. A lardunan Shanxi, Hebei, Mongoliya ta gida, Jilin da Heilongjiang, manoma da yawa sun samun wayewar kai sun kama hanyar samun kudin shiga ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha.

Duk da haka kuwa, ana ci gaba da gamuwa da matsaloli da dama a kokarin yaki da jahilci. Yayin da yake yin jawabi a ranar yaki da jahilci ta duniya a shekarar 2009, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi nuni da cewa, kawo yanzu dai yara miliyan 75 na kasa da kasa suna rasa damar shiga makarantu, yayin da matasa sama da miliyan daya suka bar makarantu ba tare da sun kammala ba. Baligai kashi daya bisa biyar ba su da kwarewar yin karatu da rubutu, mafi yawansu mata ne. Bayan haka, Ban Ki-moon ya yi nuni da cewa, kwarewar karatu na da alaka sosai da samun daraja, zarafi da kuma samun kyakkyawar makoma. A sabili da haka, Ban Ki-moon ya yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa, kungiyoyin kasashen duniya, da kungiyoyin jama'a da su kara alkawarta, da kuma samar da kayayyakin da ake bukata, a kokarin samun hakikanin ci gaba ta fuskar yaki da jahilci.

Bisa kokarin kasa da kasa baki daya, aikin yaki da jahilci ya samu babban ci gaba. Bisa alkaluman da kungiyar UNESCO ta bayar, an ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, yawan baligai masu karancin ilmi ya ragu da kimanin miliyan 40, yayin da yawan mutanen dake iya karatu ya karu daga 76% zuwa 84%.

Yayin da yake tabo dangantakar dake tsakanin "Yaki da jahilci da kiwon lafiya", Ban Ki-moon ya nuna cewa, karancin ilmi ya yi babbar illa ga lafiyar mutane. Dalilin da ya sa haka shi ne idan mutum ba ya iya karatu, ba zai iya karanta umarnin dake jikin kwalabar magani ba. Dadin dadawa, kila ne mutum ba zai fahimci hakikanin halin da ake ciki dake shafar cutar kanjamau, malariya da dai sauransu. A sakamakon hakan, Ban Ki-moon ya jaddada cewa, a kokarin cimma burin raya kasa da MDD ta tsara a shekarar 2000 na kiwon lafiyar mata masu juna biyu, da yaki da cutar kanjamau da malariya, dole ne a gudanar da aikin yaki da jahilci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China