in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana'antun kasar Sin na kokarin raya sabbin sana'o'in zamani
2010-12-06 16:22:45 cri
Ibrahim: "Sabbin Muhimman Sana'o'in Zamani" wata sabuwar kalma ce ta fuskar tatttalin arzikin kasar Sin a halin yanzu. A gun bikin cinikin sabbin fasahohin zamani na kasa da kasa da aka rufe karo na 12 a birnin Shenzhen na kasar Sin a ran 21 ga watan Nuwamba, masana'antu da yawa sun yi nune-nunen sabbin fasahohin zamani da kayayyakin da suka kera ta hanyar amfani da sabbin fasahohin zamani sabo da suna fatan su yi amfani da wannan dama ta neman ci gaba bisa sabbin muhimman sana'o'in zamani. Amma, malam Sanusi, yanzu ina da wata tambaya, wato a ganin al'ummar kasar Sin, mene ne ma'anar sabbin muhimman sana'o'in zamani? Kuma wane irin masana'antu ne suke ciki?

Sanusi: Alhaji Ibrahim, wannan tambaya ce mai kyau. A ganin al'ummar kasar Sin, sabbin muhimman sana'o'in zamani sun kunshi masana'antu masu tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da sabbin fasahohin watsa labarai da ilimin tsirrai da masana'antar da ke samar da na'urorin zamani da sabbin makamashi da sabbin kayayyaki da abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi da dai sauransu. Yanzu galibin jama'a sun dauka cewa, ba ruwansu da irin wadannan kayayyaki. Amma Mr. Tan Sui, wani jami'in kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, "Jama'a da yawa sun dauka cewa, sabbin muhimman sana'o'in zamani sun kunshi fasahohin zamani ne kawai, kamar su na'urorin zamani da jiragen sama da dai makamatansu, wato ba su fahimta ba. Amma a hakika dai, galibinsu suna da nasaba da harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Alal misali, wani kamfani ya yi nune-nunen wata sabuwar na'urar motsa jiki wadda ke iya samar da wutar lantarki, wato lokacin da ake motsa jiki a kan wannan na'ura, za ta iya samar da wutar lantarki da za a iya cajin wayar salula ko na'urar MP3."

Ibrahim: Bikin baje kolin nune-nunen kayayyakin zamani da a kan shirya a birnin Shenzhen bikin baje koli ne mafi shahara wajen nune-nunen kayayyakin zamani a kasar Sin. Yawan baki 'yan kasuwa mahalarta bikin da aka shirya a bana ya kai fiye da dubu 2 wadanda suka fito daga yankuna da kasashe 49, kuma suka zo da sabbin shirye-shirye fiye da dubu 12. Game da wannan biki, Mr. Yuan Baocheng, mataimakin magajin birnin Shenzhen ya ce, "An fi mai da hankali kan yadda ake nune-nunen kayayyakin zamani wadanda suke da nasaba da sabbin muhimman sana'o'in zamani da kuma tattaunawa kan yadda za a raya sabbin muhimman sana'o'in zamani a gun wannan biki."

Sanusi: Kamfanin samar da kayayyakin zamani na Hanwang dake kera na'urorin karatu irin na zamani ya samar da wata sabuwar na'urar karatu a gun wannan biki. Mr. Chen Ya, babban mai ba da taimako ga shugaban hukumar direktocin kamfanin Hanwang yana mai cewa, "Mun fara nazarin wannan sabuwar na'ura ce shekara daya da ta gabata. Kuma za mu fito da sabbin na'urorin karatu na zamani a kasuwannin duniya a karshen bana. Dalilin da ya sa har yanzu ba mu fitar da ita ba shi ne muna taka tsan-tsan kan nazarin sabbin kayayyaki."

Ibrahim: Wannan jami'in kamfanin Hanwang yana ganin cewa, na'urorin karatu na zamani kayayyaki ne marasa gurbata muhalli, kuma suna samun karbuwa daga wadanda suke amfani da su. A hakika dai, yanzu kayayyakin zamani marasa gurbata muhalli kuma masu inganci sun fi samun karbuwa a kasuwa. Alal misali, kamfanin kera motoci kirar BYD yana samar da kananan motoci da kayayyakin hawa masu aiki da sabbin makamashi. Mr. Yi Zemin, wani babban jami'in wannan kamfani ya ce, yawan motoci masu aiki da sabbin makamashi da kamfaninsu ya sayar a kasuwa cikin watanni 10 da suka gabata na bana ya riga ya kai fiye da dubu dari 2. Mr. Yi ya ce, "Yanzu muna kokarin yada tambarinmu a kasuwa cikin sauri. Gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufofin ba da tallafin kudi a kokarin nuna goyon baya ga motoci masu aiki da sabbin makamashi kuma marasa gurbata muhalli da muke kerawa. Alal misali, yawan tallafin kudin da gwamnatin birnin Shenzhen ta samar wa kowace mota kirar F3 da kamfaninmu ya kera ya kai kudin Sin yuan dubu 80. Sakamakon haka, ina da imani cewa, tabbas ne sana'ar kera motoci masu aiki da sabbin makamashi za ta samu ci gaba cikin sauri a nan gaba." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China