in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin sun samu ci gaba ne sakamakon gwajin da aka yi cikin shekaru 20 da suka gabata
2011-03-08 09:39:59 cri
Ibrahim: A ran 24 ga watan Nuwamba na shekarar 1986, Mr. John Phelan, shugaban hukumar direktocin kamfanin hada-hadar kudi na New York ya kwankwashi kofar ofishin cinikin takardun hannun jari na Jing'an dake birnin Shanghai na kasar Sin domin musayar ikon mallakar wata takardar hannun jari, wato takardar hannun jari ta farko ta sabuwar kasar Sin. Marigayi Deng Xiaoping ne ya ba shi wannan takardar hannun jari kyauta.

Sanusi: Bayan shekaru 4, wato a shekarar 1990, aka kafa kasuwannin hada-hadar kudi a biranen Shanghai da Shenzhen. Alamarin da ya bude kofar kasuwannin hada-hadar kudi a sabuwar kasar Sin. Amma sabo da kasar Sin tana bin tsarin gurguzu, a yi ta ce-ce-ku-ce kan batun raya kasuwannin hada-hadar kudi a kasar Sin. Game da wannan batu, marigayi Deng Xiaoping, wanda shi ne mutumin da ya tsayar da kudurin bude kofar kasar Sin ga kasashen waje da yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar, ya tabbatar a shekarar 1992 da cewa, "Takardun hannun jari da kasuwar harhadar kudi, suna da kyau ko ba su da kyau, ko za su kawo mana hadari, ko kuma abubuwa ne da suke kasancewa a kasashe masu bin tsarin jari hujja kawai, ko za a iya yin amfani da su a wata kasa mai bin tsarin gurguzu? Ya kamata mu yi nazari kan wadannan tambayoyi da kaka ambata a sama, amma dole ne mu yi gwaji don ganin tasirin tsarin ko akasinsa."

Ibrahim: Bayan an fara raya kasuwannin hada-hadar kudi a kasar Sin, kwamitin sa ido kan kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin ya soma yin gyare-gyare kan ikon mallakar takardun hannun jari. Duk wanda yake da takardun hannun jari yana iya sayar da su a kasuwa. Mr. Zhang Guojiang wanda ke nazarin takardun hannun jari a wani kamfanin kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Wani muhimmin lamarin da ya auku a kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin a shekarar 2010 shi ne an yi gyare-gyare kan ikon mallakar takardun hanun jari. Sakamakon wannan gyare-gyare, za a iya saya da kuma sayar da dukkan takardun hannun jari a kasuwa, kuma dukkan wadanda suke da takardun hannun jari matsayinsu guda ne."

Sanusi: Malam Ibrahim, wani abu mai muhimmanci shi ne a cikin gajeren lokaci, kasuwannin harhadar kudi na kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri a cikin gajeren lokaci sakamakon ayyukan gwaji da gyare-gyare da kokarin da aka yi don kyautata su. Ko da yake gwamnatin kasar Sin ta ce, shekarar 2010 shekara ce mafi sarkakiya ta fuskar tattalin arziki. Amma an fito da alkalaman dake bayyana yadda kasuwannin hada-hadar kudi za su kasance a nan gaba da harkar hada-hadar takardun hannun jari a daidai lokacin da ake bukata, wannan ya alamta cewa, kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin ta samu ci gaba sosai. Shehun malami Zhao Xijun, wanda ke nazarin harkokin tattalin arziki da takardun hannun jari a jami'ar jama'a ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, irin wannan gyare-gyare zai yi tasiri sosai ga kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin, inda Mr. Zhao yana mai cewa, "Samar da kalaman kasuwar harhadar kudi ta kasar Sin ya wadata da kuma kyautata tsarin kayayyakin da muke samarwa a kasuwar harhadar kudi ta kasar. Bugu da kari, masu zuba jari sun samu wani kayan aiki na magance afkuwar hadari sakamakon raguwar alkalaman dake bayyana yadda takardun hannun jari suke samu sauyawa a nan gaba."

Ibrahim: Sai dai malama Sanusi, lokacin da aka bude kasuwar hada-hadar kudi ta Shanghai yau shekaru 20 da suka gabata, kamfanoni 14 ne kawai suka samu izinin sayar da takardun hannun jari a kasuwar, amma ya zuwa yanzu yawan kamfanonin da suke sayar da takardun hannun jari a kasuwar ya kai fiye da dubu 2. Sannan jimillar darajar kamfanonin da suke sayar da takardun hannun jari a kasuwar harhadar kudi ta Shenzhen ta kai kudin Sin yuan biliyan dubu 27, wato ta hau kan matsayi na biyu a duniya. A cikin jawabin da Mr. Shang Fulin, shugaban kwamitin sa ido kan kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin ya yi a kwanan baya, an gane cewa, kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa sosai wajen bunkasa tattalin arzikin kasa cikin shekaru 20 da suka gabata. Mr. Shang ya ce, "Masu zuba jari za su iya samu moriya sakamakon bunkasuwar kamfanoni, sannan an damka kudaden da aka karba a hannun jama'a ga hannun amintattun kamfanoni a kokarin kara karfin kasar Sin wajen bunkasa kasuwannin hada-hadar kudi."

Sanusi: malam Ibrahim kana da labarin cewa, lokacin da kasar Sin take samu moriya sakamakon bunkasuwar kasuwannin hada-hadar kudi, har ma jama'a sun samu moriya sakamakon bunkasuwarsu. Domin bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu yawan Sinawan da suke zuba jari a kasuwannin hada-hadar kudi ya kai miliyan 130. Madam Li Jing wadda ke aiki a wani gidan talibijin a nan birnin Beijing tana daya daga cikinsu. Ko da yake a farkon lokacin da ta fara saya da kuma sayar da takardun hannun jari, ta kan fuskanci wasu matsaloli, amma yanzu ta soma samun nasara a kasuwar. Madam Li Jing ta ce, zaman rayuwarta ta sauya sosai sakamakon harkar sayar da takardun hannun jari, inda ta ce, "Yanzu yawan kudin da na samu a kasuwar harhadar kudi ya kai kai kudin Sin yuan dubu 5 a kowane wata, wato ya kai wajen rabin albashina. Sun kasance kudin kyauta ne da na samu."

Ibrahim: Lallai wannan magana ce mai dadin ji, malam Sanusi. Bugu da kari, kamfanonin kasar Sin wadanda suke cinikin takardun hannun jari a kasuwa sun kuma samu moriya sosai a cikin shekaru 20 da suka gabata sakamakon bunkasuwar kasuwannin hada-hadar kudi. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, jimillar jarin da kamfanoni suka samu a kasuwannin hada-hadar kudi na kasar ta kai kudin Sin yuan biliyan 3500, kuma yawan basusukan da suka karba a kasuwa ya kai kudin Sin yuan biliyan 2400.

Sanusi: Alal misali, yanzu kamfanin Sunning wanda ya fi girma a kasar Sin wajen sayar da injunan lantarki, ko da yake karamin kamfani ne a da. Bayan da ya samu izinin sayar da takardun hannun jari a kasuwa yau shekaru 6 da suka gabata, yawan ribar da ya samu ya karu cikin sauri kwarai. Mr. Zhang Jindong, shugaban hukumar direktoci na kamfanin Sunning ya tabbatar da muhimmiyar rawar da kasuwar hada-hadar kudi ta taka wajen bunkasa kamfaninsa, inda ya ce, "Yaya za a kafa tsarin samun bayanai game da hidimomin sufurin kayayyaki da kuma zamanintar da hanyoyinmu na tafiyar da kamfaninmu, hanya mafi kyau ita ce sayar da takardun hannun jari a kasuwa domin neman jarin da muke bukata."

Ibrahim: Amma malam Sanusi, ka san cewa, ba ma kawai kasuwannin hada-hadar kudi ta kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin takarar kamfanonin kasar Sin a kasuwa ba, har ma sun zama muhimman dandamalin daidaita tsarin tattaln arzikin kasar Sin da kyautata tsarin sana'o'in masana'antun kasar.

Sanusi: haka ne, malam Ibrahim. Lokacin da kasuwannin hada-hadar kudi na kasar Sin suke samun ci gaba cikin sauri a cikin shekaru 20 da suka gabata, a kan gamu da hadarurruka da suka jibanci wannan harka. Sakamakon haka, gwamnatin kasar Sin ta kafa kwamitin sa ido kan kasuwannin hada-hadar kudi da wani kwamitin kula da takardun hannun jari a shekarar 1992 a kokarin tabbatar da ci gaban kasuwannin hada-hadar kudi kamar yadda ake fata. Sannan kasar Sin ta fito da "dokar takardun hannun jari" a shekarar 1998 domin tsayar da matsayin kasuwannin hada-hadar kudi a kasar. A kwanan baya, Mr. Shang Fulin, shugaban kwamitin sa ido kan kasuwannin takardun hannun jari na kasar Sin ya ce, za a ci gaba da kafa dokoki ta fuskoki 5 a nan gaba a kokarin bunkasa kasuwannin hada-hadar kudi a kasar Sin bisa doka. Mr. Shang ya nuna cewa, "Kasuwannin hada-hadar kudi su kan shafi muhimmiyar moriyar jama'a kai tsaye. Sakamakon haka, ana fatan a bunkasa su cikin adalci. Har yanzu kasuwannin hada-hadar kudi na kasarmu, wato sabbin kasuwannin hada-hadar kudi ne dake neman sauye-sauye. Kuma babu isassun dokokin tafiyar da su kamar yadda ya kamata. Sabo da haka, dole ne hukumomin kafa dokoki da hukumomin sa ido su kara mai da hankali wajen kafa dokokin bunkasa kasuwannin hada-hadar kudi." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China