in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa sun nuna babban yabo ga kasar Sin wajen ba da gudummawa ga duniya
2011-03-20 14:51:06 cri
Jama'a masu karanta, yaya aiki? Yaya gida? Mun yi farin ciki domin kuna ci gaba da sauraronmu. Da fatan za ku kara samun nishadi da ilmi daga shirye-shiryenmu. A ran 11 ga wata, an yi girgizar kasa mai tsanani a kasar Japan, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu da yawa suka bace ko ji rauni. Bayan abkuwar wannan mummunan bala'i, kasa da kasa sun ba da gudummawa nan take, kamar Amurka, Koriya ta Kudu da dai sauransu. A madadin gwamnatin kasar Sin, firaminista Wen Jiabao ya jajantawa gwamnatin Japan da jama'ar kasar. A ran 12 ga wata, kungiyar Red Cross ta Sin ta ba da kudin agaji na yuan miliyan daya ga kungiyar Red Cross ta Japan. Sassa daban daban na kasar Sin kuma sun fara nuna damuwa kan lamarin cikin yakini. Bari mu yi fatan alheri ga dukkan jama'ar kasar Japan, da fatan za su yi nasarar jurewa wannan bala'i tun da wuri. Muna nuna musu goyon baya a ko da yaushe! Allah ya kara taimakawa, amin.

Jama'a masu karanta, a makon jiya mun samu sakwanni da dama daga wajenku masu sauraronmu. Ga wannan sako daga malam Salisu Dawanau a Nijeriya, inda yake bayyana cewa, "Cikin wannan mako, yayin da ake tsakiyar taruka biyu na kasar Sin, duniya baki daya, an zuba idanu da kuma kunnuwa domin ganewa da kuma sauraren abubuwan da za a tattaunawa. Musamman matsaya kan batutuwa masu nasaba da ci gaban kasar Sin, da kuma masu nasaba da hulda da wasu kasashen Duniya. Mu masu saurare, muna jin batutuwa da yawa daga bakunan jami'an da alhakin abin ke wuyan su. Sun shaida wa duniya zahirin abubuwan dake gudana. Za mu ci gaba da saurare, nan gaba za mu yi kokarin yin bayani game da abubuwan da muka fahimta game da bunkasuwar da kasar Sin ke samu, musamman idan muka yi amfani da dukkan rahotannin da jami'ai suka gabatar."

To, mun gode, malam Salisu Dawanau. Lallai, tarukan biyu na da muhimmanci sosai ga kasar Sin, inda a kan tattauna abubuwan da suka fi ba da tasiri ga rayuwar jama'a. Muna fatan kasar Sin za ta kara samun ci gaba a duk fannoni. Da fatan ku masu sauraronmu za ku kara mai da hankali kan kasar Sin.

Bayan haka, malam Yahuza Aliyu a jihar Taraba, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "Mu masu sauraronku ne, kuma hakika muna jin dadin irin yadda kuke watsa shirye-shiryenku. Muna yin muku fatan alheri."

To, mun gode, malam Yahuza Aliyu. Mun yi farin ciki domin samun amincewa daga wajenka. A nan gaba, za mu kara kokari domin samar da shirye-shirye masu kayatarwa. Da fatan za ka kara mai da hankali. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

A kwanan baya, an kammala taruka biyu na kasar Sin. Masana daga kasa da kasa suna ta kara mai da hankali kan babban sakamakon da kasar Sin ta samu wajen samun bunkasuwa. Kuma dukkansu sun nuna babban yabo ga kasar wajen ba da gudummawa ga duniya ta hanyar samun ci gaba cikin lumana.

Darektan cibiyar nazari kan kasar Sin ta hukumar nazari ta Koriya ta Kudu ya bayyana cewa, "Tare da karuwar tasirin Sin a duniya, kasa da kasa sun fara kara dora muhimmanci kan muryar da aka samu a tarukan biyu. Kasar Sin tana kan matsayi na farko wajen yin cinikayya da Koriya ta Kudu, kana wata muhimmiyar makwabciyarta. A sabili da haka, Koriya ta Kudu tana mai da hankali sosai kan tarukan biyu na kasar. Kuma kasar Sin da take samun dauwamammen ci gaba mai dorewa, za ta ba da taimako ga kasar Koriya ta Kudu. A sabili da haka, kamfanonin Koriya ta Kudu suna fatan samun bunkasuwa bisa sakamakon manyan kasuwannin kasar Sin."

Shugaban kamfanin sha'anin hada-hadar kudi na Rasha, Aleh Shvartsman ya furta cewa, "Samun ci gaban kasar Sin zai ba da taimako ga kasar Rasha. Rasha za ta ci gajiyar lamarin. Ta hanyar yin amfani da dangantakar abokantaka a fannin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, Rasha za ta kara samun jari daga kasar Sin, tare da kafa yankin musamman a fannin tattalin arziki a iyakar kasar Rasha da dai sauransu."

Darektan cibiyar duniya ta hukumar nazari kan tattalin arziki da siyasa a duniya ta asusun shugaban kasar Kazakhstan na farko Tulieshaofu ya bayyana cewa, "kasar Sin ta samu sakamako mai kyau ta hanyar samun ci gaba cikin lumana. Ko da yake kasar Sin wata babbar kasa ce, kuma tana taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya na tattalin arziki da siyasa, amma ba ta nuna fifiko, kuma ba ta yi barazana ga kowace kasa. Wannan yana da muhimmanci sosai. Kasar Sin ba ta taba nuna kiyayya ga kowace kasa bisa karfi ba. Kuma bisa kokarinta, yanayin Asiya da Pasifik mai tsanani ya samu sassauci."

Shugaban hukumar nazari kan batun kasar Sin ta jami'ar 'yanci ta Brussels Gustave ya bayyana cewa, "Shirin sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da gwamnatin kasar Sin ta dauka ya taka rawar a zo a gani wajen farfado da tattalin arzikin duniya."

Zaunannen sakataren ma'aikatar tsara fasali a shekarar 2030 ta Kenya Edward Sambili ya furta cewa, "Manufar da kasar Sin take dauka na kaucewa sa hannu cikin harkokin gida na sauran kasashen duniya ta yi kyau kwarai. Wannan ya tabbatar da tsaron jama'ar kasar dake zaune a ketare, tare da tabbatar da cewa, mafi yawan kasashen duniya suna sada zumunci da kasar Sin."

Adel Sabri, babban edita na wata jaridar Masar, ya furta cewa, "Kasar Sin ta kan tsara kyakkyawan shirin samun ci gaba, wanda ya taimaka wajen bunkasa zamantakewar al'umma lami lafiya. Ana fatan kasar Sin za ta kara hada gwiwa da kasashen Afirka, tare da taimaka musu wajen samun ci gaba daidai kamar yadda kasar Sin take yi."

Lallai yanzu kasar Sin tana samun ci gaba cikin sauri. Haka kuma tana jawo hankalin kasa da kasa baki daya. Muna fatan bayan tarukan biyu, kasar Sin za ta ci gaba da kokari wajen kara kyautata ingancin rayuwar jama'a, da kiyaye muhalli, da ba da gudummawa ga kasashen duniya da dai sauransu.

Bayan haka kuma, kwanan nan, mun sami sakwannin gaishe-gaishe daga wajen malam Muhammad Sani Gazas Chinade a Nijeriya, da malama Hauwa Isah a Sokoto, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba sabo da karancin lokaci, amma muna godiya a gare ku, kuma Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

To, jama'a masu karanta, muna fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu na Amsoshin wasikunku domin samun ilmi da nishadi, da fatan za ku kara aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayoyi da ba da shawarwari masu kyau. Yanzu iyakacin shirinmu ke nan, Fatima ke cewa da alheri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China