in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba cikin shekaru 5 masu zuwa
2011-04-01 20:45:14 cri
Garba: A farkon wannan shekara, motoci masu aiki da batura guda 50 wadanda ba sa bukatar man fetur suka soma aiki a matsayin motocin haya a titunan garin Yanqing dake wajen birnin Beijing. Wannan ya alamta cewa, sannu a hankali yanayin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba ya soma bayyana a zaman rayuwar Sinawa. A cikin shekaru masu zuwa, wadannan motoci masu aiki da batura da suke a matsayin alamu na bunkasar tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba za su yi tasiri sosai ga rayuwar jama'a.

Sanusi: Game da dalilin da ya sa ake kokarin raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, Mr. Wang Chuanfu, wato shugaban kamfanin BYD inda ake samar da motoci masu aiki da batura, kuma yake kan gaba wajen yin nazari da kuma kera motoci masu aiki da sabon makamashi ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yanzu kasar Sin na fuskantar wani hadari mai tsanani na rashin man fetur. Bayan da masana'antun kera motoci suka samu ci gaba cikin sauri a bara, a cikin shekaru 20 masu zuwa, za a tabbatar da ganin kowane iyali ya samu mota daya. Akwai iyalai miliyan dari 4 da suke zaune a kasar Sin, to, za a bukaci motoci miliyan dari 4. Idan kowace mota ta yi amfani da man fetur ton 2 cikin shekara daya, to, za a bukaci man fetur ton miliyan dari 8 a kowace shekara a nan gaba. Shi ke nan, kasar Sin ba za ta iya samar da man fetur mai tarin yawa kamar yadda ake bukata ba. Sakamakon haka, yanzu batun man fetur yana da nasaba da tsaron kasarmu."

Garba: canza salon raya tattalin arziki na yanzu, da kuma samar da sabon makamashi maras gurbata muhalli ga masana'antu, wannan ya zama burin da ake son cimmawa a duk duniya lokacin da ake kokarin raya tattalin arziki. A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta hanzarta daukar matakan bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Sabo da haka, a ganin wasu masana, sabon shiri na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin da aka zartas a yayin taron shekara-shekara na majalisar kafa dokokin kasar Sin, shiri ne na bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Sannan a cikin rahoto kan ayyukan da gwamnatin ta yi, Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya sanar da babban burin da kasar Sin za ta yi kokarin cimma cikin shekaru 5 masu zuwa a fannonin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da yin amfani da sabon makamashi, inda Mr. Wen ya ce, "A cikin shekaru 5 masu zuwa, yawan sabon makamashin da za mu yi amfani da shi zai karu, kuma zai kai kashi 11.4 cikin kashi dari bisa na jimillar makamashin da za mu yi amfani da shi. Sannan yawan abubuwan da kan jawo dumamar yanayin duniya da mu kan fitar zai ragu da kashi 17 cikin kashi dari, kuma yawan muhimman abubuwa masu gurbata muhalli da za mu fitar zai ragu da kashi 8 zuwa kashi 10 cikin kashi dari. "

Sanusi: amma, malam Garba, ta yaya ne kasar Sin za ta iya mayar da wadannan adadi su zama na gaskiya a nan gaba?

Garba: malam Sanusi, wannan wata kyakkyawar tambaya ce. Game da wannan tambaya, Mr. Zhang Ping, shugaban kwamitin kula da harkokin yin kwaskwarima da neman ci gaban kasar Sin ya bayyana wa wakilan majalisar dokokin kasar Sin matakan da gwamnatin za ta dauka a nan gaba, inda ya ce, "Lokacin da muke aiki, za mu dauki matakan da suka dace. Alal misali, daidaita tsarin na'urorin tattalin arziki da rage amfani da injuna iri na da, da kuma kayyade bunkasar masana'antu masu fitar da abubuwa da kan gurbata muhalli sosai, kuma suke amfani da makamashi kwarai. Sannan, za mu kara yin kokarin bunkasa sabbin masana'antu da sana'o'in ba da hidima."

Sanusi: Game da kokarin da gwamnatin kasar Sin ke yi, shehun malami Xin Ming wanda ke aiki a jami'ar koyar da ilmin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya ce, a cikin sabon shiri na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, gwamnatin na nuna goyon baya da tallafawa sabbin masana'antu sosai. Mr. Xin ya ce, "Wannan ne karo na farko da aka tabbatar da ma'anar tattalin arziki maras janyo gurbatar muhalli a bayyane a cikin wata takardar gwamnatin tsakiya, sabbin makamashi da tsimin makamashi da kare muhalli da ilimin tsirrai da masana'antar da ke samar da na'urorin zamani dukkansu sun zama sabbin masana'antun da za a bunkasa su a cikin shekaru 5 masu zuwa bisa sabon shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin. Haka kuma, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai a jere a kokarin nuna goyon baya da tallafawa wadannan masana'antu."

Garba: A hakika dai, ko da yake a cikin 'yan shekarun nan ne kasar Sin ta fara kokarin bunkasa tattalin arziki maras jawo gurbatar muhalli, amma ta samu ci gaba sosai. Ya zuwa shekarar 2010, yawan injunan samar da wuta masu aiki da karfin iska ya kai matsayi na farko a duk duniya gaba daya. Haka kuma, yawan injuna masu aiki da hasken rana da kasar Sin take amfani da su yana kan gaba a duniya. Bugu da kari, bisa shirin bunkasa sabbin masana'antu da sabbin makamashi da kasar Sin ta tsara, tun daga shekara ta 2011 zuwa ta 2020, jimillar kudin da kasar za ta zuba kan tasoshin samar da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa, karfin iska, hasken rana da ilmin tsirarai za ta kai kudin Sin yuan biliyan dubu 5. Babban burin da take son cimmawa shi ne yin amfani da sabbin makamashi wajen biyan bukatun zaman rayuwar jama'a.

Sanusi: Amma, malam Garba, ko da yake kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri sosai wajen bunkasa tattalin arziki maras jawo gurbatar muhalli a cikin 'yan shekarun nan, amma idan an kwatanta ta da kasashen Amurka da na Turai da ma Japan, bambancin dake akwai a tsakaninsu a bayyane yake sosai. Sabo da haka, shehun malami Xin Ming ya kara da cewa, kasar Sin tana da nauyi a kanta kwarai wajen bunkasa tattalin arziki maras jawo gurbatar muhalli, inda Mr. Xin ya ce, "A hakika dai, bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba ya zama wajibi a gare mu. Amma yanzu muna fuskantar matsin lamba sosai. Ana bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma bisa matakai daban daban, yanzu kasar Sin tana dogara da manyan masana'antu iri daban daban kawai wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma. Amma yanzu galibin kasashen yammacin duniya ba su dogara kan irin masana'antun, sakamakon haka, ba su bukatar fitar da dimbin abubuwa masu gurbata muhalli."

Garba: madam Chen Fengying wadda ke nazarin tattalin arzikin kasa da kasa tana ganin cewa, kasashen duniya na kokarin lalubo hanyoyin yin amfani da sabbin makamashi iri iri yanzu, manyan tsare-tsare ne da suke yi a kokarin raya tattalin arziki bayan da mai yiyuwa makamashin man fetur ya kare a nan gaba. Amma idan suna son samun nasara, dole ne sai sun kirkiro sabbin fasahohin da suke dacewa. Madam Chen ta ce, "Abin da ya fi muhimmanci shi ne kirkiro sabbin fasahohi, dan kwal, man fetur, man gas za su iya karewa. Sabo da haka, kamar yadda Hausawa suke fadin cewa, gidaje biyu maganin gobara, dole ne an tsara wani shiri na kirkiro sabbin fasahohin zamani dan lalubo sabbin makamashin da za su iya maye gurbin makamashi na dauri. Yanzu kasashen duniya, ciki har da kasashen Amurka da na Turai da Japan da kasar Sin dukkansu sun nuna cewa, matsala mafi tsanani dake gabansu wajen lalubo sabbin makamashi ita ce kirkiro sabbin fasahohin zamani da suke dacewa."

Sanusi: a cikin wannan takarar bunkasa tattalin arziki maras gurbata muhalli da ake yi a tsakanin kasa da kasa, kirkiro sabbin fasahohin zamani ya zama abu mafi muhimmanci, amma rashin fasahohin zamani matsala ce mafi tsanani ga kasar Sin. Mr. Chen Yong, shugaban cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta lardin Guangdong yana ganin cewa, "Fasahohin da kasar Sin ke da su yanzu fasahohi ne da kasashen duniya suka kirkiro a shekarun 70 na karnin da ya gabata. Alal misali, a cikin fasahohin da suke nasaba da sana'o'in kiyaye ingancin muhalli, yawan fasahohin da suke da nasaba da sana'o'in ba da hidima ya kai kashi 50 cikin kashi dari, sannan kasashen Japan da Amurka da na Turai suke da galibinsu. A ganina, dole ne mu kirkiro mu kuma mallakar fasahohi daidaita batutuwan sabbin makamashi da muhalli da kanmu, har ma mu ba da irin wannan hidima da kanmu. Idan ba haka ba, lallai wadannan batutuwa za su kawo illa ga tsaron kasar da kuma rayuwar jama'a gaba daya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China