in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tasirin ayyukan kungiyar Amnesty International 
2013-09-01 19:21:20 cri

Amnesty International ko AI a takaice, kungiya ce mai zaman kanta, wadda wani lauya dan asalin kasar Birtaniya mai suna Peter Benenson ya kafa a shekarar 1961, burin ta shi ne daukar matakan doka wajen kare hakkokin bil'ad ta ama musamman ma hakkokin al'ummomin da basu da galihu. A yanzu haka wannan kungiya tana da mambobi da magoya baya da yawansu ya kai mutum miliyan 3 a kasashe da yawansu ya haura 150.

Wannan kungiya ta shahara matuka wajen gudanar da bincike, da fidda rahotanni kan halin da al'ummomin dake fuskantar cin zarafi, ko take hakki ke fuskanta a duk fadin duniya. Bugu da kari Amnesty International na gabatar da shawarwari,kudurori na daukar matakan doka ga MDD kan mahukunta, kungiyoyi, ko gwamnatocin da ake zarginsu da aikata laifuka masu alaka da take hakkin al'ummar fararen hula a lokutan yaki, ko ma bisa dalilai na siyasa.

Sau da yawa akan ji irin wadannan rahotanni a kafofin watsa labaru na kasa da kasa, irin rahotannin da a wasu lokuta ke sanya manyan kungiyoyi ko hukumomin duniya, dama na shiyyoyi daukar matakan shiga tsakani, ko bada kariya ga wadanda aka, ko ake kokarin dannewa hakki.

A takaice dai ayyukan wannan kungiya sun fi bada karfi a fagagen kare yancin mata, kananan yara, masu rangwamen gata da kuma marasa galihu. Kungiyar na kuma taka rawar gani a yunkurin da wasu kungiyoyi ke yi na haramta aiwatar da hukuncin kisa, da bada kariya ga 'yan gudun hijira, kare hakkin fursunoni, da kuma goyon bayan duk wasu matakai na kare mutunci da darajar dan adam.

Kokarin da wannan kungiya ta yi wajen yaki da azabtar da mutane da ake zargi da aikata laifuffuka, yasa a shekarar 1977, ta samu lambar yabo ta "Nobel", wadda aka kebe musamman ga wadanda suka bada gudummawa a fannin aikin wanzar da zaman lafiya. Har ila yau, ta samu lambar karramawa ta MDD, bisa aikinta na kare hakkokin bil'adama a shekarar 1978.

Koda yake dai Amnesty International ta samu yabo daga sassan manazarta ayyukanta, da masu fashin baki kan harkokin da suka jibanci kare hakkokin bil'adama, a hannu guda, wasu manazarta na ganin bakinta, duk da cewa yadda take taka rawa wajen goyon bayan ra'ayin wani sashe na kasashe masu fada a ji, wanda hakan a wasu lokuta, ke sanyawa a cusa siyasa, da son rai a cikin irin rahotannin da take fitarwa. Hakan ne ma ya sanya a shekarar 1980 kasar Rasha ta zarge ta da laifin leken asiri, a kuma shekarar 1983 mahukuntan kasar Argentina suka haramta amfani da rahotan da ta fitar a dukkanin fadin kasarsu, baya ga suka da tasha daga mahukuntan kasar Morocco dake kallonta a matsayin mai bada kariya ga masu aikata laifuffuka.(Ibrahim/Saminu/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China