in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar malamai ta kasar Sin
2013-09-21 16:24:40 cri


Ranar malamai ko "Teachers Day" a Turance, rana ce da kusan dukkan kasashen duniya suke kebewa don bitar irin rawar da malamai suka taka, matsalolinsu, nasarorin da suka cimma ko nuna yabo ga irin babbar gudummawar da suka bayar a bangaren ci gaban ilimi.

Ko da ya ke kowace kasa da ranar da ta kebe da kuma irin shagulgulan da a kan shirya don murnar wannan rana. Yayin da a wasu kasashen ake shirya taruka da gabatar da jawabai, a wasu kasashen kuma, dalibai ne kan baiwa malaman nasu kyaututtuka don nuna masu godiya da yabo saboda ilimin da suka ba su.

Sai dai duk da gudummawar da aka san malamai suna bayarwa ga ci gaban kowace al'umma, har yanzu wannan sana'a ta malanta na fuskantar koma baya, ma'ana ba ta da daraja a wannan lokaci, sakamakon abin da masana ke dangantawa ga rikon sakainar-kashin da mahukunta ke yiwa sana'ar.

Masu fashin bakin na cewa, kamata ya yi hukumomi su samar da muhimman abubuwan da sanar'ar malanta ke bukata, matakin da ake ganin zai haifar da 'da mai ido ga shi kansa bangaren na ilimi da a yanzu ya ke fuskantar matsala a galibin kasashe masu tasowa. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China