in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar yaki da Jahilci ta duniya
2013-09-16 19:27:20 cri

A ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar 1965 ne kungiyar kula da harkokin Ilimi, kimiyya da ala'adu ta MDD (UNESCO) ta tsaida ranar 8 ga watan Satumban kowace shekara a matsayin ranar yaki da jahilci, ko da ya ke an yi bikin farko na wannan rana ce a shekarar 1966.

Manufar shirya wannan biki ita ce, ilimantar da jama'a da daukacin alumma fa'idar iya karatu da rubutu, ma'ana yaki da jahilci kamar yadda aka fi sani a galibin kasashen Afirka.

Alkaluma sun nuna cewa, akwai kimanin mutane miliyan 775 da har yanzu ba su iya karutu da rubutu ba, sannan cikin mutane 5 akwai mutum a kalla guda da ake jin bai iya karatu da rubutu ba, kana kashi 2 bisa uku cikin wannan adadi da muka ambata na wadanda ba su iya karatu da rubuntun ba mata ne.

Sai dai masana na danganta wannan matsala ta jahilci ko rashin iya karatu da rubutu da batun talauci, al'ada da rashin ingantattun manufofi ko tsare-tsare a bangaren hukomomin irin wadannan kasashe da abin ya shafa.

Masu fashin baki na cewa, rashin magance wannan matsala ta jahilci, tana iya haifar da tarin matsalolin daka iya shafar bangarorin tattalin arziki, Ilimi, lafiya da sauran muhimman sassan ci gaban kasa. (Ibrahim/Sanushi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China