in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ran 1 ga watan Oktoba, rana ce ta murnar kafuwar sabuwar kasar Sin da samun 'yancin Najeriya
2013-10-03 16:04:14 cri


Ranar 1 ga watan Oktoban kowa ce shekara, rana ce da Sinawa ke murnar ranar da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949.

A wannan rana ce da Sinawa karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), suka ayyana nasarar 'yantar da kasar, bayan gwagwarmaya, inda aka shirya gagarumin biki a dandalin Tian'anmen.

Yayin wannan biki ne shugaban kasar Sin na wancan lokaci Mao Zedong, ya ayyana kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin, inda ya daga tutar kasar ta farko da kansa, kana bayanai suka nuna cewa, sojoji da jama'a kusan 300,000 ne suka yi jerin gwano a bikin.

Tun wannan lokaci ne kasar Sin take bunkasa a fannoni dabam-dabam, har zuwa yanzu da ta kasance kasa mai karfin tattalin arziki a duniya.

Saboda muhimmancin wannan rana ne, ya sa gwamnatin kasar Sin ta kebe mako guda cur a matsayin ranakun hutu, inda 'yan kasar Sin ke amfani da wannan lokaci don ziyartar wuraren shakatawa tare da kai ziyara ga 'yan uwa da abokan arziki.

Bugu da kari, a wannan rana ce wato 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, ita ma Najeriya, babbar abokiyar kasar Sin a fannin cinikayya, ta samu nata 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya, inda nan ma ake shirya shagulgula don murnar wannan rana tare da bitar irin nasarorin da gwamnatocin wadannan kasashen suka samu ya zuwa wannan lokaci da kuma sassan da ke bukatar kara ingantawa. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China