in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar kalubaloli sosai wajen yakar matsalar abinci a duniya
2013-11-28 16:12:24 cri


Ana bikin wannan rana ce a ranar 16 ga watan Oktoban kowa ce shekara don karrama ranar da aka kafa kungiyar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) da aka yi a shekara ta 1945.

Kasashe mambobin shirin na FAO ne suka kafa wannan rana a babban taron kungiyar karo na 20 a watan Nuwamban shekarar 1945.

Tun wannan lokaci ne, yayin da ake bikin wannan rana, ake bullo da taken da zai kasance a shekarar, misali yakar yunwa don rage talauci ko zuba jari a bangaren aikin gona don kara samar da abinci da sauransu.

Wani rahoto da shirin samar da abinci na duniya (WFP) ya fitar, ya nuna cewa, a yanzu haka akwai mutane kimanin miliyan 870 a duniya da ke fama da matsalar yunwa, ko da yake matsalar ta ragu idan aka kwatanta da shekara ta 2009.

Bugu da kari, masana sun bayyana cewa, akwai gibi sosai a tsakanin burin rage rabin yawan mutanen da ke fama da yunwa a shekara ta 2015 da MDD ta gabatar, kana akwai rahotannin da ke nuna cewa, saboda karuwar yawan jama'a a duniya, yawan bukatar abinci a duniya a shekara ta 2050 za ta karu da kashi 60 cikin 100 bisa na yanzu.

Wannan ne ya sa masana ke ganin cewa, akwai bukatar mahukunta, kungiyoyin kasa da kasa da sauran jama'a da su tashi tsaye wajen zana manufofi da shirye-shirye a kokarin ganin an warware matsalar abinci da ake fuskanta a duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China