in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar Kiwon Lafiya ta Duniya
2014-04-22 15:59:53 cri

Ranar 7 ga watan Afirilun kowace shekara, rana ce da aka kebe domin tunawa da kafuwar hukumar lafiya ta duniya wato WHO a shekarar 1948, kimanin shekaru 66 da suka gabata ke nan.

Taken bikin na bana shi ne "yaduwar cututtuka ta hanyar kananan kwari masu illa". An kuma yi amfani da wannan take a bana wajen wayar da kan al'ummar duniya, su fahimci tasirin da irin wadannan halittu kamar su sauro da dangoginsa ke da su wajen yada cututtuka. Don haka ne ma aka yada sakon dake cewa "Sauro, da Kuda, da dangoginsu hadari ne ga rayuwarka da ta iyalinka, yayin da kake gida ko a halin tafiya".

Kowa dai ya san yadda sauro ga misali ke yada kwayoyin cututtuka, kamar zazzabin cizon sauro, da ma wasu cututtuka da masana ke cewa an gano suna yaduwa ne ta hanyar sauro. Cututtuka irinsu zazzabin shawara, da ciwon dundumi da dai sauransu duka misali ne na wadannan cututtuka.

Bugu da kari rahotannin da hukumar WHO ke fitarwa sun nuna cewa, irin wadannan cututtuka suna haddasa mutuwar mutane da dama ciki hadda yara kanana 'yan asalin nahiyar Afirka. An kuma yi ittifakin yaduwar irin wadannan cututtuka na da nasaba da mu'amala da cudanyar al'ummomin duniya daban daban, sakamakon tafiye-tafiye da makamantansu. Haka kuma akwai batun tasirin yanayi ta yadda ga misali wurare masu zafi ke kasancewa wurin kyankyasar irin wadancan kwari masu illa.

Cikin karin matakan da ake fatan dauka akwai bayyanawa matafiya hanyoyin da za su bi wajen kare kansu daga kamuwa da cututtuka makamantan wadannan.

A 'yan shekarun nan, hukumomin kasa da kasa da na kasashen daban daban, na ci gaba da hadin gwiwa wajen yakar tasirin irin wadannan cututtuka dake hallaka dubban al'ummun duniya.

Kuma rahotannin baya bayan nan da hukumar lafiya ta duniya ta fitar sun nuna cewa, an samu gagarumar nasarar dakile yaduwar cutar shan-inna wato Polio, ko da yake akwai cututtukan da gurbatacciyar iska ke haifarwa, da tarin TB, da cutar sankara, wadanda ke barazana ga yunkurin da kasashen duniya ke yi na yaki da cututtuka. Baya cutar Ebola da a baya bayan nan ke ciwa wasu kasashen Afirka tuwo a kwarya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China