in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmmancin taron CICA ga zaman lafiya da wadatar duniya
2014-05-27 08:29:11 cri

A ranar Talata 20 ga watan Mayu ne aka bude taron inganta cudanya da hadin gwiwa a nahiyar Asiya (CICA) a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin.

Manufar wannan taro, ita ce magance cece-kucen da wasu kasashen Asiya ke yi game da ikon mallakar iyakokinsu da sauran muhimman batutuwa da ke shafarsu.

An kaddamar da wannan taro ne da yanzu haka ya kunshi kasashe 24 a shekara 1992, wanda ya kasance wani dandalin da ya kunshi bangarori da dama dake ba da zarafin tattauna harkar tsaro.

Baya ga wadannan kasashe mambobi, akwai kasashe 'yan kallo guda 9, wadanda suka hada da Bangladesh, Sri Lanka, Phillipines, Japan, Malaysia, Qatar, Ukraine da Amurka. Sai kuma kungiyoyin kasa da kasa guda 4 da suka hada da MDD, OSCE da kungiyar hada kan kasashen Larabawa.

Masana na ganin cewa, taron na CICA zai taimaka wajen kulla aminci da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban-daban, saboda muhimmanci ko tasirinsa, musamman idan aka tabo batun arewa maso gabashin nahiyar, wato Sin, Japan da Koriya ta kudu, kasashe ne da aka fara samun kirkire-kirkire, kuma kasashe ne da tattalin arziki da zaman al'ummarsu ke saurin bunkasa.

Bugu da kari, wadannan kasashe 24 da ke cikin wannan taro na CICA na da al'umma da yawanta ya zarce kashi 90 cikin 100 na al'ummar Asiya haka ma filayensu. Wannan ya sa baban sakataren MDD Ban Ki-moon da ya halarci taron, ya ce, yana fatan shugabannin yankin Asiya da Fasifik za su inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki ta hanyar yin shawarwari.

Masu fashin baki na bayyana cewa, karni na 21 zai kasance wani zamani na Asiya, shi ya sa Ban Ki-moon shi ma ya ce, muddin ana fatan cimma wannan buri, wajibi ne kasashen na Asiya su kara hada kai da juna.

Ana fatan abubuwan da za a tattaunawa a wannan taro su taimaka wajen warware matsalolin da kasashen yankin na Asiya da ma sauran sassan duniya ke fuskanta.

Kuma kamar kullum, buri da manufar kasar Sin, shi ne samun duniya mai kwanciyar hankali da wadata. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China