in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Illar ayyukan ta'adanci ga ci gaban kasa
2014-05-28 20:59:10 cri

A 'yan kwanakin nan 'yan ta'adda, 'yan a ware da masu kiran kansu masu tsattsauran ra'ayi suna ta kara aikata munanan abubuwa, kamar yin garkuwa ko kai hare-haren da ke shafar fararen hula da ba su san hawa ba balle sauka a sassa daban-daban na duniya, lamarin da ke kara haifar da matsalar tsaro a tsarin zamantakewar al'umma.

Baya ga sauran matsaloli da ayyukan irin wadannan bata gari ke haifarwa, ayyukan ta'addancin na kuma zubar da martabar kasa a idon duniya baya ga koma bayan da za ta iya samu a dukkan fannoni.

A kokarin da kasar Sin take yi na kakkabe ayyukan 'yan ta'adda ya sa a kwanakin baya ma'aikatar tsaron jama'ar kasar ta kira wani taro da nufin bullo da wani tsari na musamman na tsawon shekara da zai kai ga murkushe ayyukan ta'addanci a kasar.

Matakan da kasar Sin da sauran kasashen da ke fama da matsalolin 'yan ta'adda suka dauka sun samu yabo daga masu fashin baki. Sai dai, baya ga matakan da kasashen ke dauka, akwai bukatar su ma al'ummomi su bayar da tasu gudummawar ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Manazarta na ganin cewa, kamata ya yi gwamnatoci a dukkan su kasance masu adalci, tare da samar wa matasa ayyukan yi, matakan da ake ganin za su kara taimakawa wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci da suka kasance ruwan dare gama duniya.

A hannu guda kuma, kamata ya yi su ma masu aikata wannan danyen aiki, su kasance masu kishin kasa su daina aikata wannan mummunan aiki na rashin tausayi su koma cikin al'umma tare da bayar da tasu gudummawar da ta dace don gina duniya mai zaman lafiya, karko da wadata don amfanin kowa da kowa. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China