in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mu ga yadda baki suke fahimtar yanayin Beijing
2014-06-30 10:41:03 cri

A ranar 5 ga watan Yuni, ranar kare muhalli ta duniya ce. Bari mu ga wani bayani da na rubuta dangane da hirar da na yi da wasu baki, wadanda suke zama a nan birnin Beijing.

Tare da zuwan lokacin zafi, an samu kyautatuwar iska a Beijing, amma a ranar 5 ga watan Yuni wato ranar kare muhalli ta duniya, jama'a da yawa sun kara mai da hankali kan halin da ake ciki ga iskar Beijing, musamman ma baki da zuka zo daga kasa da kasa, su ma sun fi mai da hankali kan iskar Beijing.

Bayan da wani 'dan kasar Pakistan mai suna Ghani ur Rehman ya iso nan Beijing, ya ji mamaki, sabo da yanayin Beijing ya sha bamban sosai da na kasarsa. Ya ce,

"Gurbacewar iska a kasar Pakistan ba ta fi tsanani ta nan Beijing ba. Idan aka kwatanta Sin da Pakistan, ana iya ganin cewa, Sin ta kasance wata kasa mai tasowa, wadda take gina ayyuka da yawa, wadda kuma take da masana'antu da kamfanoni masu yawan gaske, kasar Sin kuma tana cikin yunkurin zama wata kasa irin ta masana'antu. Bayan da na iso nan Beijing, na ga ya kasance da gurbacewar iska a kwanaki biyu ko uku a cikin wani mako guda, ba safai a kan ga sararin sama mai launin kore ba, wani lokaci kuma hasken rana ya ratsa gurbacewar iska da wuya, ya kasance da wasu kananan kayayyaki masu guba a cikin iska."

Game da hanyar da yake bi wajen tinkarar gurbacewar iska a Beijing, Mista Ghani ur Rehman ba ya dabara mai kyau. Ya ce,

"Idan akwai gurbacewar iska, sai na zauna a gida, na kulle taga, ban fita waje ba. A Beijing, kana iya ganin mutane da yawa suna sanya marufi hanci, don magance gurbacewar iska, amma ni yanzu ban saya ba, babban dalili shi ne akwai wuyar numfashi yayin sanya marufin hanci."

Amma wani malami da ya zo daga kasar Bangladesh mai suna Enamul hoque Tutul yana da wata dabara wajen tinkarar kalubale daga gurbacewar iska. Ya ce,

"Na ga wani abu mai ban sha'awa, a wani karo, na ga wani kare ya sanya marufi hanci, wannan dai da wuyar fahimta, ina tsamanni cewa, dalilinsa shi ne gurbacewar iska. Daga nan kuma ni na shirya wani marufi hanci, idan akwai gurbacewar iska, yayin na fita waje, sai na sanya marufi hancin."

Game da hanyoyin da ake bi wajen kawar da gurbacewar iska a Beijing, 'dan kasar Bangladesh mai suna Enamul hoque Tutul ya nuna yabo ga matakan da Beijing ya dauka, a sa'i daya kuma, ya gabatar da shawarwarinsa. Ya ce,

"A ganina, tilas ne mu samu jituwa da hallitu. Mu taki sa'a ne sabo da yanzu mutane da yawa sun riga sun gano illar daga gurbacewar muhalli. A halin yanzu dai akwai tarurruka a duniya da ke magance gurbacewar muhalli. Beijing shi ma ya dauki matakai da dama wajen kare muhalli, kamar babban bas da ke amfani da makamashi mai tsabta, irin wannan bas ba zai haddasa gurbacewar iska ba. A wani bangare daban kuma, a ganina, ya kamata mu inganta kawar da gurbacewar muhalli kamar ma'adinnai na kwal da dai sauransu. Kamata ya yi mu dinga yin abubuwa da yawa da ba su haddasa gurbacewar muhalli ba, don kare muhalli namu." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China