in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ka sani game da wasan Taichi?
2014-06-14 21:00:37 cri

Taijiquan da aka fi san shi da wasan Taichi wani nau'in wasan Kungfu na gargajiya na kasar Sin ne, wanda ke iya taimakawa kiwon lafiyar jikin mutum tare kuma da sanya mutum natsuwa. Taichi bai tsaya ga wasa kawai ba, amma wani muhimmin bangare ne na al'adun al'ummar kasar Sin da ke ba da karin haske a kan ainihin al'adun kasar Sin da basirar al'ummar kasashen gabas.

A cikin 'yan shekarun baya, wasan Taichi ya fara samun karbuwa sosai a kasashen duniya da dama. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu haka akwai mutane fiye da miliyan 150 da ke wasan Taichi a duniya baki daya.

Garin Handan ya kasance wani muhimmin wurin da aka fara samun asalin wasan, don haka ne ake kiransa garin wasan Taichi. Tun daga shekarar 1991, garin na Handan ya fara gudanar da dandalin wasan Taichi na kasa da kasa, dandalin da ke janyo masu sha'awar wasan da kwararrun wasan a kowace shekara. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China