in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin da EU ke shirin dauka game da bakin haure
2015-05-28 15:46:59 cri

Hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Turai ta EU tana shirin bullo da wani shirin rarraba baki 'yan ci-rani da ke shigowa nahiyar tsakanin kasashe mambobin kungiyar 28.

Hukumar EU ta ce, ta dauki wannan mataki ne don ganin an kawo karshen halakar da 'yan ci-ranin ke yi a tekun Bahar-Rum a kokarin da su ke yi na neman shiga Turai ko ta halin kaka.

Sai dai wannan mataki bai yiwa wasu kasashe mambobin kungiyar irin su Denmark,Holland da Burtaniya dadi ba, Inda suka ce su kam ba za su lamunci wannan tsari ba, yayin da ita kuma kasar Jamus ta yi maraba da wannan shiri.

Baya ga batun rarraba baki 'yan ci-ranin da kungiyar EU ke shirin gabatarwa har ila kungiyar ta ce, za ta lalata duk wani kwale-kwale da aka kama a tekun Bahar-Rum dauke da baki 'yan ci-rani. Shi ma wannan shiri na EU ya gamu da suka daga kasar Libya wadda ta ce ba a tuntube ta ba kafin a dauki wannan mataki, don haka ba ta amince da shi ba.

Kasar ta Libya ta kafa hujjar cewa, ta ya ya za a tantance tsakanin kwale-kwale na gaskiya da wanda ke dauke da agajin jin kai ko masu fataucin bakin haure?

Irin wadannan bakin haure dai na barin kasashensu na asali ne sakamakon tashin hankali ko matsalar tattalin arziki ko wasu nau'o'in bala'u daga indallahi da nufin shiga turai ko za su fita daga irin wannan kangi.

Bayanai na nuna cewa, mutane da dama ne ke rasa rayukansu a teku a kowa ce shekara a kokarin shiga Turai ta kwale-kwale marasa inganci.

Alkaluman baya-bayan nan sun bayyana cewa, sama da bakin haure 60,000 ne suka yi kokarin shiga Turai a wannan shekara kadai.

Masu fashin baki na ganin cewa,hanya daya tilo ta magance wannan matsala ta 'yan ci-rani da ke kokarin shiga Turai ita ce, kamata ya yi gwamnatocin kasashen da bakin bakin hauren ke fitowa su inganta rayuwar al'ummominsu maimakon rubda da ciki da kudaden jama'a da aka damka musu amana. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China