in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama kasa ta farko a duniya da za ta shirya wasannin IOC na zafi da na sanyi
2015-08-13 08:52:55 cri

A ranar Jumma'a 31 ga watan Yulin shekarar 2015 ne mambobin kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya IOC, suka zabi biranen Beijing da Zhangjiakou na kasar Sin a matsayin biranen da za su dauki bakuncin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022.

Ko da yake, birnin Alma-Ata na kasar Khazakstan bai samu wannan dama ba, kafofin yada labaru daban-daban na kasar sun darajanta ayyukan da birnin Beijing ya yi, kuma sun amince da cewa, birnin Beijing zai samu nasarar shirya wannan gasa saboda ganin nasarar da ya samu a shekarar 2008.

A cewar shugaba Xi Jinping na kasar Sin, bisa burin da ake da shi na shirya gagarumar gasa mai kayatarwa, wadda za ta dace da burin al'ummar Sinawa biliyan 1.3, gwamnati za ta cika alkawuranta, za kuma a cimma babbar nasarar da ake fata da hadin kan dukkanin al'umma, da goyon bayan kasashe, da shi kansa kwamitin na IOC, ta yadda hakan zai zamo dama ta yada manufar gasar wasannin Olympics a duniya.

Masu fashin baki na ganin cewa, bayanan da kasar Sin ta gabatar na neman daukar bakuncin wannan gasa, manufofi ne da al'ummun yankunan za su dade suna cin gajiyarsu a bangarorin tattalin arziki, sufuri, cinikayya da makamantansu. Yanzu haka, kasar Sin ta kasance kasa ta farko a duniya da ta samu damar shirya gasar wasannin Olympics na lokutan zafi da kuma sanyi a tarihin kwamitin na IOC na sama da shekaru 100. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China