in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitaccen tarihin sabon ma'aikacinmu-Ahmed Inuwa Fagam
2015-08-27 12:04:48 cri

An haifi Ahmad Inuwa Fagam ne a garin Fagam dake karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa a tarayyar Najeriya. Ya halarci kwalejin nazarin shari'a da addinin Islama dake Misau a Jihar Bauchi daga shekarar 1997 zuwa 1999, inda ya samu karamar Diploma

Ya samu digirinsa na farko a jami'ar Maiduguri a fannin aikin jarida daga shekarar 2003 zuwa 2007, sannan ya samu digiri na biyu a fannin magance faruwar annoba da harkokin ci gaba a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria (ABU) daga shekarar 2011 zuwa 2013.

Ya fara aiki a gidan radio Freedom mai zaman kansa dake Dutse a jihar Jigawa a shekarar 2009 zuwa 2013, daga nan ya yi aiki na watanni 6 a sashen Hausa na BBC a ofishinsu dake Abuja daga watan Satumba na shekarar 2013 zuwa watan Maris na 2014.

Daga bisani sai ya koma BBC Media Action da aka fi sani da BBC World Service Trust daga Agustan 2014 zuwa Satumban 2015. Ya kuma halarci kwasa–kwasan aikin jarida a wurare da lokuta daban-daban kafin ya fara aiki a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin (CRI). (Ibrahim Yaya, Sanusi, Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China