in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna nan kasar Sin (2)
2015-12-03 20:58:21 cri

A sakamakon yadda huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ke dinga yaukaka, da kuma yadda hadin gwiwarsu ke dada habaka a fannoni daban daban, al'ummar sassan biyu ma suna kara cudanya da juna. A nan kasar Sin, 'yan Afirka da ke zuwa sai karuwa suke yi cikin 'yan shekarun baya bayan nan. Cikin su akwai masu zuwa domin harkokin kasuwanci, ko dalibta, ko kuma wadanda ke zuwa domin gudanar da sauran ayyuka. A daya bangaren kuma akwai ma wadanda ke zama su tara iyalai a nan kasar Sin.

Alhaji Sani Tsoho Alhassan na daya daga mazauna kasar Sin wadanda suka dade, wanda sakamakon zaman sa a kasar ta Sin har ma ya auri wata Basiniya, kuma suka haifi 'ya'ya.

Sani Tsoho Alhassan dan kasuwa ne da yanzu haka yake gudanar da harkokinsa a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin. Ya kuma fara zuwa birnin ne a karshen shekarar 2005, wato yau kimanin shekaru 10 ke nan.


 

Malam Sani yana tare da wani bako a ofishinsa. Sani ya dade yana kasuwanci a nan kasar Sin, don haka, baki da sukan zo daga gida, su kan sauka wurinsa in suna bukatar wani kaya, inda shi kuma ke yin iyakacin kokarin biyan bukatunsu.

 

A wajen shekarar 2007 ne, malam Sani ya hadu da wata basiniya mai suna Zhong Liangxing, wadda kuma daga baya aka sa mata sunan Halima, kuma sannu a hankali suka fada cikin soyayya.

 

A shekarar 2012, masoyan sun yi aure, kuma sun gudanar da bikin aure a garinsu malam Sani, wato birnin Kano, dake tarayyar Nijeriya.

Daga baya, sun haifi 'ya mace, kuma aka sanya mata suna A'isha. Malama Halima ke nan tare da diyarta A'isha.

Malama Halima tana yin sallah tare da mijinta. Bayan sun yi aure, malama Halima ta musulunta bisa son ranta, kuma ta kan yi sallah kamar yadda musulmi ke yi a kowace rana.

Bayan da malam Sani ya zo kasar Sin, wani lokaci ya kan yi kewar abincin gargajiya na Hausawa. Don haka, bayan da suka yi aure, malama Halima ta yi kokarin koyon girke-girke irin na Hausawa, ciki har da dan wake da mijinta ke so.

Malam Sani ya kuma bude wani kamfani na kansa, inda ake kera kayan gini na kwanon rufi, kuma kayayyakinsa na samun karbuwa sosai, "mun gode Allah, ciniki ya na kyau, ina da baki da suke zuwa daga Ghana, da Nijer, da Mali, da Guinea, da kuma Angola da Zambiya."

Malam Sani yana tare da wani bako daga Nijeriya da ya zo neman kayan gini.

Malam Sani yana tare da ma'aikata a kamfaninsa.

Yanzu A'isha ta kai kimanin shekaru uku, ga shi kuma a wannan shekara, Allah ya kara musu wata jaririya, kuma aka rada mata suna Ha'uwa.

Malam Sani ya ce, Allah ya albarkace shi da 'ya'ya biyu, wadanda suke da jinin Afirka da ma na kasar Sin, idan sun girma, yana so ya tura su zuwa Nijeriya, don su kara fahimtar al'adun Afirka, kuma su zama gadar sada zumunta a tsakanin sassan biyu.

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China