in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari ya cika shekara guda cif a kan karagar mulkin Najeriya
2016-06-17 16:00:55 cri

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2016 da muke ciki ne, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya cika shekara guda cif na karagar mulki, bayan da ya lashe zaben shugaban kasar da ya gabata wanda ya janyo hankulan duniya sakamakon halin da kasar ta shiga na mummunan matsalar tsaro da kuma yadda hare-haren mayakan Boko Haram suka yi kusan durkusar da kasar baki daya.

Bugu da kari, Najeriya ta tsinci kanta cikin wasu tarin matsaloli, wadanda suka hada da matsalar karancin hasken wutar lantarki, da rashin aikin yi tsakanin matasan kasar, da rikicin addini da na kabilancin da kuma uwa uba matsalar cin hanci da ta zama ado a kasar.

Sai dai a lokacin da yake yakin neman zabe, shugaba Buhari ya sha alwashin kawo karshen wadannan matsaloli da suka yi wa kasar daurin kazar kuku. Sai dai wasu masu fashin baki na ganin cewa, dukkan nasarorin da jami'an tsaron kasar ke cewa suna samu a kan mayakan Boko Haram, wannan tamkar baya ba zane ne, domin a daya bangaren kuma matsalar sace mutane ana garkuwa da su domin neman fansa da kuma yadda tsagerun yankin Niger Delta ke ci gaba da fasa bututan mai a yankin na ci gaba da tsananta.

Haka za kila, yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki shi ma batu ne da ke damun 'yan kasar, lamarin da masana ke cewa, ya faru ne sakamakon faduwar farashin mai da kasar ta dogara a kai a kasuwannin duniya da kuma yadda ake fasa na'urorin kamfanonin hakar mai a yankin Niger Delta da sauransu.

Masu sharhi na cewa, shugaba Buhari ya taka rawar gani a fannonin inganta tsaro da kuma manufofin gwamnatinsa na samar da ayyukan yi ga matasan kasar. Don haka, kamata ya yi 'yan kasar su kara yin hakuri tare da baiwa shugaban goyon baya da karin lokaci, ganin irin tarin matsalolin da ya gada da kuma halin da duniya ke ciki ta fuskar tattalin arziki. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China