in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaddamar da ke tsakanin Sin da Philippine kan tekun kudancin Sin
2016-07-21 17:15:58 cri

A ranar Talata 12 ga watan Yulin shekarar 2016 ne wata kotun kasa da kasa da ke Hague ta yanke hukunci kan karar da kasar Philippine ta shigar bisa radin kanta dangane da takaddamar da ke tsakaninta da Sin kan batun tekun kudancin kasar Sin.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, ba ta amince ba kuma ba ta yarda da sakamakon hukuncin da kotun ta yanke bisa bukatar Jamhuriyar kasar Philippine kan batun tekun kudancin kasar Sin ba.

A ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2013 ne, tsohuwar gwammatin Jamhuriyar kasar Philippine bisa radin kanta ta shigar da kara game da takaddamar da ke tsakaninta da kasar Sin game da batun tekun kudancin Sin. Amma a ranar 19 ga watan Fabrairun shekarar 2013, gwamnatin kasar Sin ta ayyana cewa, ba ta amince da wannan mataki na kasar Philippine ba, kuma ba za ta halarci zaman kotun ba, kuma tun wannan lokaci ta sha nanata wannan matsayin da ta dauka kan wannan batu.

A ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2014, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takarda wadda take bayyana matsayinta game da hurumin kotun da kasar Philippine ta kirkiro game da wannan batu, tana mai bayyana cewa, matakin da kasar Philippine ta dauka ta neman kafa wannan kotu ya sabawa yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, sannan ya keta yarjejeniyar teku ta MDD, da kuma baki dayan ayyukan shiga tsakani na kasa da kasa, kuma wannan kotu ba ta da 'yancin yanke hukunci kan wannan batu.

Matakin da kasar Philippine din ta dauka na gabatar da wannan batu a gaban kotu, ko kadan bai dace ba. Kuma hakan ba zai taimaka wajen warware takaddamar dake tsakanin Sin da Philippine ba, ko kuma ya taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin. Haka kuma wani yunkuri ne na take 'yancin mallakar yankuna da teku na kasar Sin da kuma muradunta a yankin tekun kudancin kasar. Bugu da kari, kafa wannan kotu bisa bukatar Philippine shi kansa ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Masana na bayyana cewa, kamata ya yi a bar kasashe da ke da 'yanci su warware takaddamar da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa, maimakon tsoma baki daga wani bangaren da wannan batu bai shafa ba daga dukkan fannoni. Domin hukuncin kotun da yadda ta tafiyar da wannan batu, ya sabawa ayyukan sasantawa na kasa da kasa, kuma ya kauce daga dalilin kafa dokokin teku na MDD har zuwa yadda ake kokarin sassanta takaddama cikin lumana, kuma wannan mataki ya take 'yancin kasar Sin na mallakar yankunanta. (Ahmed/Ada/Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China