in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Ghana sun tashi zuwa birnin Rio
2016-08-02 16:28:17 cri
'yan wasan kasar Ghana, karkashin tawagar kasar ta tashi daga birnin Accra a ranar Lahadi a kan hanyar ta ta isa birnin Rio na kasar Brazil, inda za su shiga gasar Olympics ta bana.

Hukumar kamfanin man fetur ta kasar Ghana GNPC, ta raka 'yan wasan domin yin ban kwana da su, a filin saukar jiragen sama, a wani mataki na ci gaba da tallafawa, da samar da kudin gudanarwa da kamfanin ke baiwa 'yan wasan, a shirin su na wakiltar kasar wajen halartar wasannin na Olympics na wannan karo.

Kungiyar 'yan wasan kasar ta Ghana dai a wannan karo, na kunshe da 'yan wasa matasa da yawa, a cewar Francis Dodoo, shugaban kwamitin Olympics na kasar, kuma matsakaitan shekarun 'yan wasan bai wuce 22 ba, cikin su hadda 'yan wasa 16, wadanda wannan ne karon farko da suke halartar gasar. Kaza lika Ghana na fatan samun nasara a gasar, bayan kwashe shekaru 24 bata samu nasarar lashe lambar Zinari ba a gasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China