in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata bayyana sabon kociyan Super Eagles a watan Augusta
2016-08-02 16:30:34 cri
Jami'ai a Najeriya sun bayyana cewa, hukumar gudanarwar kwallon kafa ta kasar zata bayyana sunan jami'in da zai jagoranci horas da 'yan wasan babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles a cikin watan Augusta mai zuwa.

Chris Green, shine shugaban kwamitin kwararru, da tsare tsare a hukumar kwallon kafa ta kasar (NFF), ya kuma tabbatar da hakan ga manema labaru a Abuja, fadar mulkin kasar.

Tuni dai kwamitin gudanarwar hukumar ya baiwa kwamitin kwararrun wa'adin kwanaki 7 da ya bayyana mutumin da zai zamo babban jami'in horas da 'yan wasan babbar kungiyar kwallonn kafan kasar, bayan da hukumar ta NFF ta gaza samun amincewar koci dan asalin kasar Faransa Paul Le Guen a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar.

Green, ya ce koda yake wa'adin da NFF ta baiwa kwamitin don ya maye gurbin Le Guen ya cika tun a ranar 27 ga watan Yuli, duk da haka ana ta kokarin daukar matakai don tabbatar ganin wa'adin bai wuce wannan wata na Augusta ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China