in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IOC zai binciki kalaman batanci da Horton ya yi a kan abokin hamayyarsa na kasar Sin
2016-08-08 09:52:30 cri

Kwamitin kula da wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC ya tabbatar da cewar, zai yi bincike kan kalaman batanci da dan wasan ninkaya na kasar Australiya Mack Horton ya yi kan abokin hamayyarsa na kasar Sin Sun Yang kafin ya ce komai game da batun.

Mai Magana da yawun kwamitin na IOC Mark Adams, ya fada a jiya Lahadi cewa, ba shi da masaniya game da wannan batu, sai lokacin da manema labarai suka sanar da shi cewar, Mack Horton ya ambaci dan wasan ninkaya na mita 400 Sun Yang na kasar Sin da cewa "mai amfani da haramtattun kwayoyi masu sa kuzari", kafin fara wasan da ma bayan kammala wasannin na mita 400 a wasan karshe na Rio Olympics.

A cewa, Adams. sam bai san wannan al'amari ba, don haka zai gudanar da bincike, in ji shi. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China