in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwallon kafan Najeriya ta amince da Rohr a matsayin kociyan Super Eagles
2016-08-08 14:19:29 cri

An shawarci hukumar kula da kwallon kafan Najeriya da ta duba yiwuwar daukar Gernot Rohr a matsayin sabon mai ba da shawara ta fuskar fasaha ga 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles.

Ahmed Yusuf, mataimakin shugaban kwamitin kula da fasaha da ci gaba na hukumar harkokin kwallon kafa ta kasar NFF, ya fada wa 'yan jaridu jiya Lahadi a Abuja cewar, kwamitin ya amince da bai wa Rohr wannan mukami.

Ya ce, kwamitin ya gamsu da cancantar tsohon dan wasan baya na kasar Jamus da ya kasance mai ba da shawara ta fuskar fasaha ga 'yan wasan na Super Eagles, bayan doguwar muhawara da kwamitin ya gudanar a ranar Asabar da ta gabata a Abuja.

Yusuf ya ce, kwamitin ya gamsu matuka bisa yin nazari game da irin bajintar da Rohr ya nuna a lokacin da ya yi aiki tare da hukumar kwallon kafan kasar Jamus DFB. Ya ce, don haka suka gayyato shi zuwa Najeriya domin tattaunawa da shi.

A cewarsa, sun gano dan wasan na Jamus yana da hali na gari, da kuma kwazo wajen gudanar da aikinsa, sanna ya nuna sha'awar zama a Najeriya.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China