in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta samu gurbi a gasar nahiyar Afirka ta U-17
2016-08-24 13:31:07 cri
Kungiyar kwallon kafar kasar Ghana ta matasa 'yan kasa da shekaru 17, ta kai matsayi na gaba a wasan share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka na U-17, duk da doke ta da Burkina Faso ta yi a wasan da suka buga na ranar Asabar.

Black Starlets dai ta kwashi kashin ta a hannu, bayan da Burkina Faso ta dura mata kwallaye 4 da daya. Sai dai duk da hakan, tsiran maki daya dake tsakanin kungiyoyin biyu bisa jimillar wasannin da suka buga a baya, ya baiwa Ghanan damar buga wasa na gaba da Cote d'Ivoire a wannan zagaye.

A baya dai Black Starlets ta Ghana ta dauki kofin wannan gasa har karo biyu, a wannan karo ma 'yan wasan ta na ci gaba da kokarin samun gurbin gasar, bayan da aka dakatar da kasar bisa sanya 'yan wasa da shekarun su suka haura 17 a gasar da ta gabata.

Ghana da Madagascar da sauran kungiyoyin kasashe 6 ne za su buga gasar ta shekarar 2017 a kasar Madagascar, wadda za a fara wasannin karshe na share fagen ta daga ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China