in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An daga tutar kasar Sin a kauyen 'yan wasa nakasassu na Rio
2016-09-06 13:31:19 cri

Za a gudanar da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Rio daga ranar 7 zuwa 18 ga wata.

A safiyar ranar 5 ga wata ne 'yan wasan nakasassu na kasar Sin suka daga tutar kasar Sin a kauyen 'yan wasa a Rio.

Rong Jing, 'yar wasan takobi kan keken guragu ta kasar Sin wadda ta samu lambar zinariya a gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta London za ta rike tutar kasar Sin a yayin bikin bude gasar Rio a madadin kasar Sin.

Tawagar 'yan wasan nakasassu ta kasar Sin na kunshe da mutane 499, ciki hadda 'yan wasa 308, wadanda yawansu ya kai matsayin koli a tarihin kasar Sin a fannin halartar gasar wasannin Olympics ta nakasassu wadda aka gudanar a kasashen ketare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China