in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FIFA ta gyara yawan albashin jami'anta don ya zama dacewa da doka
2016-09-07 19:23:09 cri

Hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA, ta sanar a kwanakin baya cewa, manyan kusoshin hukumar sun cimma ra'ayi daya, game da rage yawan albashin shugaban hukumar da na babban sakataren ta. An kayyade cewa, yawan albashin shugaban FIFA zai kai kudin Switzerland Franc miliyan 1.5 a ko wace shekara, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1 da dubu 530 ke nan, yayin da na babban sakataren hukumar zai kai kudin Switzerland Franc miliyan 1.3, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1 da dubu 327.

A yanzu kuma yawan albashin na su ya ragu da rubu'I, idan an kwatanta su da albashin magabantan manyan jami'an 2. Matakin da aka dauka ya nuna niyyar hukumar FIFA, ta cika alkawarinta na gudanar da ayyukanta bisa tsari da doka, kuma ba tare da rufa-rufa ba.

Ko shakka babu al'ummar duniya ta dade ta na mai da hankali kan tsare-tsaren da ake bi wajen gudanar da hukumar FIFA, musamman ma a fannin harkar kudi, ganin yadda hukumar ke samun makudan kudin shiga ta hanyar hada kasuwanci da wasan kwallon kafa, amma rashin wani managarcin tsari na sa ido a kan ta, musamman ma tabargazar cin hanci da rashawa da wasu manyan jami'an hukumar suka aiwatar, ta sa an zurawa batutuwa masu alaka da hukumar ido, ciki har da batun albashin manyan jami'anta.

Yadda ake mai da hankali kan hukumar FIFA, ya sa ta zartas da wani shirin kwaskwarima kan tsarin aikinta a farkon wannan shekara, shirin da ya kunshi matakin tabbatar da yawan albashin manyan jami'an hukumar, gami da bayyana su a fili. Saboda haka hukumar ta kafa majalisar tsara shirin da ya shafi albashin ma'aikatanta, don gudanar da kwaskwarima, wadda kuma daga bisani ta tabbatar da yawan albashin jami'an.

Bayan da hukumar FIFA ta sanar da sabon albashin, ta ce sabbin kwantiragin da za a kulla tare da shugaba, da babban sakataren FIFA, sun dace da dokar kasar Switzerland, inda hedkwatar hukumar FIFA ke ciki, gami da ka'idojin hukumar, kuma za a nuna yawan kudin da aka ware domin biyan albashin, cikin rahoton da za a samar dangane da harkar kudi da aikin kula da hukumar. Haka zalika ita ma majalissar kula da albashi za ta sa ido kan yadda ake biyan kudin, don tabbatar da cewa ba a keta ka'idar da aka tsara ba.

Hakika yadda aka sanar da yawan albashin shugaban hukumar FIFA, da babban sakataren hukumar, ya kasance matakin farko da aka dauka bisa aniyyar hukumar ta gudanar da cikakkiyar kwaskwarima kan tsare-tsarenta. Bayan an kammala aiki na wannan mataki, za a sake duba dukkan manufofin hukumar ta FIFA ta fuskar biyan albashin ma'aikata, don neman maye gurbinsu da wasu sabbin manufofi, wadanda za a gabatar da su nan da wasu watanni.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China