in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CRCC na kasar Sin da kamfanin HBK na kasar Qatar sun samu iznin gina babban filin wasa na gasar cin kofin duniya ta 2022
2016-12-07 20:03:00 cri
Kwamitin shirya gasar cin kofin duniya ta kasar Qatar ya sanar a kwanakin baya cewa, kamfanin CRCC na kasar Sin da kamfnain HBK na kasar Qatar sun samu iznin gina babban filin wasa na gasar wasanni wato filin wasa na Lusail.

A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, shugaban kwamitin shirya gasar cin kofin duniya ta Qatar Hassan Al-Thawadi ya taya murna ga kamfanonin biyu da suka samu izinin gina filin wasa na Lusail. Ya bayyana cewa, filin wasa na Lusail daya ne daga cikin manyan filayen wasa a gasar cin kofin duniya ta Qatar, zai zama wuri mafi shahara a wannan birni, wanda zai yi maraba da masu sha'awar wasan kwallon kafa daga kasa da kasa.

Filin wasan na Lusail na da nisan kilomita 20 daga arewacin babban birnin kasar Doha, wanda zai zama babban filin wasa na gasar cin kofin duniya ta kasar Qatar da za a gudanar a shekarar 2022, inda za a gudanar da bikin bude gasar wasan farko na gasar, da wasan karshe na gasar, da bikin rufe gasar da sauransu. Bayan rufe gasar, za a yi amfani da filin wasan a matsayin wurin yin wasanni ko ayyukan raya al'adu. Bisa shirin da aka tsara, za a kammala aikin gina filin wasan a shekarar 2020.

A ranar 25 ga watan Satumba na shekarar 2015 ne, hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta tabbatar da lokacin gudanar da gasar cin kofin duniya ta kasar Qatar ta shekarar 2022, wannan ne karo na farko da za a gudanar da gasar cin kofin duniya a lokacin sanyi, wato daga ranar 21 ga watan Nuwanba zuwa ranar 18 ga watan Disamba na shekarar 2022. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China