in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka a shekarar 2016
2017-01-01 12:12:07 cri

A kowace shekara, abubuwa kan faru, kama daga na ban-al'ajabi, mamaki, tausayi, bajinta, takaici, tashin hankali da dai sauransu, haka lamarin ya kasance a wannan shekarar 2016.

Baya ga ire-iren abubuwan da muka ambata a sama da kan faru a cikin kowace shekara, a kan kuma kulla dangantaka ko kai ziyarar sada zumunci tsakanin shugabannin kasashe da nufin kara karfafa dankon zumunci ko huldar cinikayya, al'adu, tattalin arziki da dai sauransu.

A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2016 ne wasu 'yan ta'adda suka kai hari kan wani otel dake birnin Ouagadougou, fadar mulkin Barkina-Faso, inda suka halaka mutane 28, kana wasu 56 kuma suka jikkata.

A shekarar ta 2016 ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar da Gambia da kuma Ghana na baya-bayan nan. Haka kuma a shekarar 2016 da ke shirin karewa ne aka yankewa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre hukuncin daurin rai da rai bisa zarginsa da take hakkin bil-Adama a lokacin da yake mulkin kasar daga shekata ta 1982 zuwa ta 1990.

Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki a duniya baki daya a sabuwar shekarar 2017. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China