in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabriel: Ina son ci gaba da zama a Inter Milan
2016-12-28 19:10:53 cri
Dan wasan gaban kasar Brazil dake taka leda a kungiyar kwallon kafar Inter Milan ta Italiya Gabriel Barbosa, ya musanta rade-radin da ake yi cewa, wai baya farin ciki da ci gaba da kasancewar sa a kungiyar Inter Milan. Barbosa ya ce tabbas yana farin cikin kasancewa a wannan kungiyar dake buga gasar firimiyar italiya wato Serie A.

Ya ce "domin cimma buri na na kasancewa a nan, dole na yi hakuri da juriya". Ya ce watana 3 na yi kacal da zuwa nan kuma ina fatan samun damar buga wasanni masu yawa.

Barbosa ya ce salon wasa a Italiya ya banbanta da na gida Brazil, amma duk da haka yana fatan komawa kungiyar ta Milan a watan Janairu bayan hutu, domin ci gaba da buga wasanni kakar bana. Ya ce a tunanin sa idan har zai iya buga wasa a Milan yadda ya kamata, ko shakka babu zai iya buga wasa a ko ina a duniya.

Kalaman na Barbosa dai sun ci karo da na manajan sa Wagner Ribeiro, wanda a farkon watan nan aka jiyo shi na cewa, Barbosa na cikin wani hali, kasancewar ba ya samun damar buga wasanni yadda ya kamata, tun zuwan sa Inter Milan cikin watan Satumbar da ya gabata. Ya ce cikin kusan watanni 4 da ya shafe a kungiyar, wasanni 3 kacal aka bashi damar bugawa.

A baya ma dai wasu kafofin watsa labarai na Brazil sun rika hasashen cewa, mai yiwuwa ne dan wasan mai shekaru 20 a duniya ya koma tsohon kulaf din sa wato Santos, ko Atletico Mineiro, a lokacin musayar 'yan wasa na watan Janairu mai zuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China