in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Peterhansel ya zama zakaran gasar tseren motoci ta Dakar a karo na 13
2017-01-18 15:52:54 cri
Dan wasan tseren motoci daga kasar Faransa mai yiwa kamfanin Peugeot tuki Stephane Peterhansel, ya lashe Sebastien Loeb, abokin karawar sa daga kamfanin Peugeot wanda shi ma daga kasar Faransa ya fito, a gasar ranar Asabar da ta gabata, wadda aka shirya domin tseren motoci ta Dakar da ta gudana a Argentina, inda Peterhansel ya sake lashe kofin gasar a karo na 13.

Dan wasan mai shekaru 51 a duniya, ya kasance na 2 cikin matakin karshe da nisan kilomita 786 na tseren motocin da aka yi, wanda aka fara daga garin Rio Cuarto ya zuwa garin Buenos Aires. Wannan sakamako dai ya tabbatar da zamansa a matsayi na farko bisa daukacin tsawon lokacin da ya kwashe na sa'o'i 28 da mintuna 49 gami da dakikoki 30.

A nasa bangaren, Loeb ya zama na biyu, bisa karin wasu mituna 5 da dakikoki 13 da ya kwashe. Yayin da Cyril Despres, wanda shi ma yana cikin kungiyar motocin kamfanin na Peugeot, ya kasance na 3 a gasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China