in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin matakan yaki da cutar AIDS na kasar Sin
2017-02-16 14:24:11 cri

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da shirinta na rigakafin cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS na shekaru biyar wanda ya shafi rigakafi da kuma ba da magani ga masu dauke da cutar.

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta wallafa a shafinta na intanet, inda ta bayyana cewa, gwamnatin za ta yi kokarin zakulo mutanen dake dauke da kwayar cutar ta HIV, da rage hanyoyin kamuwa da cutar ta hanyar amfani da allura, da hanyar karin jini, da kuma uwa zuwa ga jaririnta. Shirin zai kuma takaita yaduwar kwayoyin cutar, da inganta lafiyar masu dauke da cutar.

Sanarwar ta ce, za'a aiwatar da wannan shirin ne tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, kuma an yi kyakkyawan tanadi na takaita hanyoyin kamuwa da cutar da suka hada da hanyar luwadi a tsakanin maza da kashi 10 cikin 100, da kuma takaita hanyoyin daukar cutar daga jikin uwa zuwa jariri da kashi 4 cikin 100.

An tsara cewa, za a baiwa sama da kashi 90 cikin 100 na mutanen dake dauke da cutar magunguna, kana sama da kashi 90 cikin 100 kuma za a yi musu maganin cutar cikin nasara.

Karkashin wannan shirin kuma za'a yi amfani da magungunan gargajiya wajen warkar da cutar ta AIDS, matakin da masana suka bayyana cewa, zai taimaka wajen kara samun karbuwar magungunan gargajiyar kasar Sin a fannin yaki da cutar kanjamau da ma sauran manyan cututtuka a duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China