in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bukaci a tabbatar da tsaron nahiyar Afrika
2017-03-24 10:42:28 cri
Wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci a dauki matakan samar da wata rundunar ko-ta-kwana wacce zata tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika.

Liu Jieyi, wanda shi ne zaunannen wakilin Sin a MDD, ya yi wannan kiran ne a lokacin taron kwamitin MDDr game da batun kasar Somali.

Mista Liu yace kasar Somali ta shiga wani muhimmin mataki na sake ginin kasar, sai dai a cewarsa har yanzu batun tsaro da yanayin bada jin kai na cigaba da zaman babbar damuwa, dadin dadawa ga yawaitar hare haren ta'addanci da matsalar fari da ke addabar kasar a halin yanzu.

Babban wakilin musamman na MDD dake Somali Michael Keating, ya fadawa taron MDD cewar sama da mutane miliyan 6 'yan kasar Somali kusan rabin al'ummar kasar ne ke bukatar gudummawa. Kusan mata da kananan yara miliyan 3 ne suke cikin bukatar gaggawa na neman ceton rayuwarsu a kasar, wannan hali ya hada da karuwar adadin mutanen dake rayuwa cikin mummunan yanayi a sansanin yan gudun hijira.

Kwamitin MDD mai mutane 15 ya amince da babban rinjaye na tsawaita wa'adin tawagar wanzar da tsaro ta MDD dake Somalia (UNSOM) har zuwa ranar 16 ga watan Yunin 2017.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China