in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a Burtaniya da kakkausar murya
2017-03-24 12:27:56 cri

Jiya Alhamis, babban sakataren MDD Antonio Guterresta ta bakin kakakinsa Farhan Haq, ya yi Allah wadai da kakkausar murya da harin ta'addancin da aka kai a birnin London na kasar Burtaniya, wannan rana kuma daukacin wakilan kasashen mambobin kwamitin sulhun MDD sun yi shiru har tsawon minti daya domin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a yayin harin ta'addancin kafin su kaddamar da zaman taron. Manzon kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya sake jaddada matsayin da kasar Sin ta dauka wajen yaki da ayyukan ta'addanci.

Babban sakataren MDD Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar murya ga harin ta'addancin da aka kai a birnin London na Burtaniya, kuma ya yi alkawari cewa, MDD za ta ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin Burtaniya da al'ummar kasar, yana mai cewa, "MDD ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a wurin dake kusa da babban ginin majalisar dokokin kasar Burtaniya, mu ma mun nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a harin da iyalansu baki daya, kana muna fatan wadanda suka ji rauni a yayin harin za su warke cikin sauri, har kullum MDD tana goyon bayan gwamnatin Burtaniya da al'ummar kasar."

Wannan rana sakataren harkokin wajen kasar Burtaniya Boris Johnson ya shugabanci taron kwamitin sulhun, inda ya sake yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a London a ranar 22 ga wata, yana mai cewa, "Kafin a kaddamar da taron kwamitin sulhun yau, a madadin daukacin kasashen mambobin kwamitin, bari in sake yin Allah wadai da mugun laifin ta'addancin da aka aikata a London a ranar 22 ga wata, mutane da dama da basu ci ba su sha ba sun rasa rayukansu a harin, wasu kuwa sun jikkata, a nan bari in isar da alhini ga iyalan wadanda suka rasa rayuka, yanzu bari mu tashi tsaye mu yi shiru har tsawon minti daya domin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a yayin harin."

Daga baya daukacin wakilan sun mike tsaye sun yi shiru har tsawon minti daya domin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a harin London.

Yayin taron, manzon kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya sake jaddada matsayin da kasar Sin ta dauka wajen yaki da aikin ta'addanci, kuma ya nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a harin, kana ya isar da alhini ga iyalan wadanda suka rasa rayuka yayin harin. Liu Jieyi ya bayyana cewa, "Gwamnatin kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a Londion a ranar 22 ga wata, mu ma mun nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a harin, kana bari mu isar da alhini ga iyalan wadanda suka rasa rayuka a harin. Aikin ta'addanci annobar daukacin kasashen duniya ce, kasar Sin ta nuna kiyayya ga aikin ta'addancin, kuma tana son kara karfafa hadin gwiwa dake tskaninta da sauran kasashen duniya domin dakile barazana da kalubale a fannin, da hakan za a kiyaye zaman lafiya a fadin duniya yadda ya kamata."

Bayan da aka kammala taron, sakataren harkokin wajen Boris Johnson ya gana da manema labarai a wajen dakin taron, inda ya nuna godiya ga kasashen mambobin kwamitin sulhun saboda juyayin da suka nuna, haka kuma ya nuna godiya ga MDD saboda alhini da goyon bayan da ta nuna. Johnson ya bayyana cewa, harin ta'addancin da aka kai a London kalubale ne da kasashen duniya ke fuskanta, shi ya sa kamata ya yiwa daukacin kasashen duniya su hada kai domin dakile ta'addanci tare. Sakataren harkokin wajen Johnson yana mai cewa, "Bisa labarin da aka samu yanzun nan, wadanda suka rasa rayuka da wadanda suka jikkata a yayin harin sun zo ne daga kasashe 11, hakan ya nuna cewa, an kai harin ne ga al'ummomin fadin duniya."

Jiya hukumar 'yan sandan birnin London ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa, mai kai harin wanda aka harbe shi da bindiga har ya mutu yana da shekaru 52 da haihuwa, sunansa shi ne Khalid Masood, an haife shi ne kasar ta Burtaniya.

A ranar 22 ga wata, Khalid Masood ya tuka wata mota ya ci karo da wasu mutane a kusa da babban ginin majalisar dokokin kasar, daga baya ya sauka daga motar tare da wata wuka, har ya kai hari ga mutane da wukar, a karshe dai, 'yan sanda suka harbe shi da bindiga har ya mutu. A sanadin haka, saura mutane 3 sun rasa rayuka a yayin harin, kusan 40 suka jikkata. Jiya ne kungiyar masu tsattsauren ra'ayi ta IS ta sanar da cewa, ta dauki alhakin kai harin na London.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China