in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya zanta ta waya da shugaban kwamitin kungiyar AU
2017-03-24 19:50:34 cri
A jiya Alhamis ne mamban a majalissar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, ya zanta ta wayar tarho da shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki, a yayin da yake ci gaba da ziyara a wasu kasashen Afirka.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin mu'amala tare da kwamitin kungiyar AU, tare da aiwatar da shirye-shirye 10 na hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da su, da tattauna kan yadda za a raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, a tsakanin bangarorin biyu bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa bangare, Mr. Faki cewa yayi, kasashen Afirka na jinjinawa kasar Sin bisa goyon bayan ta ga jama'ar Afirka, wajen warware matsalolin nahiyar ta hanyar siyasa, da samar da gudummawar ta wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya, da bunkasuwa a Afirka. Ya ce yana fatan za a koyi fasahohin Sin, a kara raya hadin gwiwa, da sada zumunta tare da kasar Sin a dukkan fannoni, don samun moriyar juna da bunkasuwa tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China