in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan gudun hijira kimanin 250 sun bace a sakamakon hadarin jiragen ruwa a kusa da gabar tekun kasar Libya
2017-03-24 20:20:42 cri
Wata kungiya mai zaman kanta ta masu aikin ceto ta kasar Sifaniya, ta bayyana cewa, ta gano jiragen ruwa biyu, masu dauke da 'yan gudun hijira, da suka kife a kusa da gabar tekun kasar Libya, kuma akwai hasashen cewa wasu mutane fiye da 250 sun bace sakamakon hadarin.

Masu aikin ceto sun bayyana cewa, yanzu haka an gano gawawwaki 5 a dab da jiragen ruwan, wadanda shekarunsu ke tsakanin 16 zuwa 25.

Kungiyar dai ta bayyana cewa, ko wane jirgin ruwa irin wadanda aka gano na daukar 'yan gudun hijira fiye da 120, don haka mai yiwuwa ne wasu mutanen fiye da 250 sun bace a sakamakon hadarin. Kuma da yake hadarin ya faru sama da kwana guda, akwai yiwuwar samun karin wadanda suka rasu sakamakon hadarin.

Ofishin kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD ya nuna matukar juyayi da aukuwar wannan lamari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China