in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya murnar budewar taron dandalin Boao
2017-03-25 09:42:49 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murna ga bikin budewar taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin Asiya, wanda ya gudana a yau Asabar, a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Cikin sakon, shugaba Xi Jinping ya ce, bayan da an kafa dandalin Boao shekaru 16 da suka wuce, ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa samun ra'ayi daya tsakanin kasashen Asiya, da habaka hadin gwiwa tsakaninsu, da daukaka matsayin nahiyar Asiya a idanun al'ummomin kasa da kasa.

A cewar shugaban, yadda aka sanya "dunkulewar tattalin arziki da ciniki cikin 'yanci" ya zama taken taron na wannan shekara na dandalin Boao, ya nuna yadda gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashen dake nahiyar Asiya, suke mai da cikakken hankali kan batun dunkulewar tattalin arzikin duniya waje daya. Shugaban kasar Sin ya ce yana fatan ganin mahalartar taron za su yi kokarin tattaunawa, tare da samar da shawarwari masu kyau ga yunkurin daidaita matsalolin da tattalin arzikin shiyya-shiyya gami da na daukacin duniya suke fuskantar, ta yadda za a samu damar kyautata manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya, don ta zama mai dorewa, wadda za ta haifar da karin moriya ga bangarori daban daban. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China